Daga karshe: An gano dalilin hauhawar fyade a Najeriya

Daga karshe: An gano dalilin hauhawar fyade a Najeriya

Pauline Tallen, Ministar kula da harkokin mata ta Najeriya ta alakanta hauhawar fyade da dokar kulle da aka saka don dakile yaduwar annobar korona a Najeriya.

Tallen ta sanar da hakan ne ga manema labaran gidan gwamnati a ranar Laraba, 10 ga watan Yunin 2020, bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya inda ta kawo matsalar fyade gabansu.

Ta bayyana cewa za a dauki mataki wanda zai hada da na shari'a da kuma kafafen yada labarai don shawo kan matsalar fyade.

"Fyade ya yawaita a yayin da ake kulle sakamakon annobar korona. Na san ana samun matsalar fyade a kasar nan amma yanzu ta fi yawaita saboda zaune da ake a gida, an rufe mata da yara tare da masu cin zarafinsu.

"Adadin ya hau da kusan kaso uku na abunda muke gani a baya. Babu jihar da aka tsame don a koda yaushe al'amarin karuwa yake.

Daga karshe: An gano dalilin hauhawar fyade a Najeriya

Daga karshe: An gano dalilin hauhawar fyade a Najeriya Hoto: Pulse.ng
Source: UGC

"Muna bukatar taimakon shari'a. Daga bayanan da muka samu, akwai daruruwan shari'u a tsakanin kotunanmu wadanda ba a magance su ba.

KU KARANTA KUMA: Harkallar filaye: Tubabben sarkin Kano Sanusi II ya daukaka kara

"A saboda haka muke kira ga kafofin yada labarai don wayar da kai. Ina son mutane su fito su bayyana halin da suke ciki.

"Wadannan sune matsalolin gida daka aka kai gaban majalisar zartarwa kuma muna farin cikin sanar muku cewa shugaban kasa na goyon baya da dukkan 'yan majalisar.

"Akwai mataki mai tsauri da gwamnati za ta dauka don bai wa mata da kananan yara kariya a kasar nan," tace.

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata kotun majistare da ke jihar Legas ta saki wata matashiyar budurwa mai shekaru 15 sakamakon kashe wani tsoho mai shekaru 51 mai suna Babatunde Ishola.

Matashiyar budurwar ta tabbatar da cewa kare kanta ta yi yunkurin yi bayan tsohon ya yi yunkurin yi mata fyade.

Mai shari'a Philip Adebowale Ojo ya soke zargin da ake yi wa matashiyar da ke aji shida na sakandare bayan shawarar da ya samu daga hukumar gurfanarwa ta jihar Legas.

Daraktan ofishin kare kai na jihar Legas, Dr. Babajide Martins ya nuna gamsuwarsa a kan hukuncin kotun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel