Fyade: An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Fyade: An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Babban kotu da ke zamanta a Igobosere, Legas a ranar Laraba ta yanke wa wasu maza biyu, Williams Udoh da Ubong Isiah hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An kuma yanke wa Udoh hukuncin shekaru 21 a gidan yari saboda yi wa matan aure fyade.

A Kano, yan sanda sun kama wani mutum mai shekaru 30 da aka ce ya yi wa kimanin mata 40 fyade a gari daya cikin shekara guda.

Kakakin yan sanda, Abdullahi Haruna ya tabbatar da kama wanda ake zargin inda ya ce wanda ake zargin, Mohammed ya amsa lafinsa.

Fyade: An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya

Fyade: An yanke wa mutum biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya. Hoto daga NLC.
Source: UGC

Ya ce wadanda ya yi wa fyaden sun hada da yan mata, matan aure da tsofaffi.

DUBA WANNAN: Allah ya yi wa hadimin Aisha Buhari rasuwa

Haruna ya ce wanda ake zargin ya shiga wani gida domin yi wa wata yarinya fyade ne amma mahaifiyarta ta yi ihu kuma hakan ya yi sanadin kama shi.

Nan ba da dade wa ba za a gurfanar da shi, in ji Haruna.

Yan sanda a jihar Benue a ranar Laraba sun kama wani likita da ake zargin ya yi wa yarinya mai shekara 11 fyade a Otukpo.

The Nation ta ruwaito cewa an dakko yarinyar ne daga kauye domin ta taya mutumin raino.

Yarinyar ta ce mutumin ya haike mata ne a lokacin da matarsa ta yi balaguro zuwa Kaduna.

"A daren ranar ya dawo gida a buge da giya kuma ya yi kokarin taba ni amma na gudu.

"A daren jiya ya sake dawowa ya dauke ni daga dakina zuwa dakinsa ya tilasta min saduwa da shi.

"Na samu rauni a gaba na, wuya na da baki na saboda gumurzun da muka yi kafin ya fi karfi na," in ji ta.

Likitan ya ce giyar da ya sha ne ta saka shi aikata mummunan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel