Buhari ya sha alwashin daukar babban mataki a kan masu fyade

Buhari ya sha alwashin daukar babban mataki a kan masu fyade

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba ya aminta da shirye-shiryen da ma'aikatar kula da harkokin mata ta fitar don shawo kan matsalar fyaden kananan yara da mata a kasar nan.

Ministar kula da harkokin mata, Pauline Tallen, yayin jawabi ga manema labaran gidan gwamnati bayan taron yanar gizo da suka gama na majalisar zartarwa, ta ce ta mika bukatar daukar mataki a kan 'annobar fyade' gaban Buhari.

Tallen, wacce ta tabbatar da cewa bukatar ta samu goyon baya daga shugaban kasa, ta ce ma'aikatarta za ta tsaurara wayar da kai ta kafofin yada labarai tare da hadin guiwa da ma'aikatar yada labarai.

Ministar ta kwatanta yawaitar fyade a fadin kasar nan da abun kunya tare da kira ga jihohi da kada su sassauta wa masu fyade ko kadan.

Ta ce a cikin jihohi 36 na kasar nan, tara ne kadai ke amfani da dokar yaki da cin zarafi.

Ta matukar sukar fyade tare da kisan Vera Uwaila Omozuwa, budurwa mai shekaru 22 da ke karantar ilimin sanin kananan halittu.

A makon da ya gabata, an yi wa Barakat Bello mai shekaru 18 fyade tare da kasheta har cikin gidansu a jihar Oyo.

Hakazalika, Azeezat Shomuyiwa mai shekaru 29 dauke da juna biyu an kasheta har lahira a gidanta da ke jihar Oyo.

Tallen, wacce ta ce 'yan majalisar zartarwar babu wata hamayya suka aminta da bukatarta, ta kara da cewa ta samu goyon baya daga wurin gwamnoni.

Buhari ya sha alwashin dauka babban mataki a kan masu fyade

Buhari ya sha alwashin dauka babban mataki a kan masu fyade. Hoto daga The Cable
Source: Twitter

KU KARANTA: Matawalle ya bawa tsohon ɗan takarar gwamnan APGA muhimmin muƙami

Ta ce: "Na san duk kun san abinda ya faru a kasar nan a makon da ya gabata. Kasar nan ta koka da annobar da ke damunmu.

"Baya ga annobar korona da ta damemu, annobar fyade ta kunno kai tare da cin zarafi.

"Da dokar hana walwala wacce annobar korona ta kawo, mata da kananan yara na kulle a gida inda ake ci gaba da cin zarafinsu.

"Na san tun kafin zuwa annobar korona, akwai matsalar fyade da musgunawa wani jinsi. Amma kullen ya kara matsalar don ta ninka a kalla sau uku."

Ta kara da cewa: "Ina farin cikin sanar muku da cewa na samu goyon bayan gwamnoni kuma sun shirya hada guiwa da ma'aikatarmu don kawo karshen annobar.

"Wannan abun tsoro ne da tozarci. Yana zubar wa Najeriya da mutunci a idon duniya. Ba za mu aminta da hakan ba."

Ministar ta ce za a saka malamai da sarakunan gargajiya cikin lamarin don wayarwa da al'umma kai.

"Muna kammala yakar korona, za mu fito tare da ma'aikatar yada labarai don bayyana illolin abubuwan da ke faruwa," tace.

Tallen ta ce cin zarafi da yi wa kananan yara fyade ya fi tada mata hankali.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel