Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade

Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade

- Kotun majistare da ke jihar Legas ta saki wata matashiyar budurwa mai shekaru 15 sakamakon kashe wani tsoho mai shekaru 51

- Ta kashe tsohon mai suna Babatunde Ishola bayan ya yi kokarin yi mata fyade

- Mai shari'a Philip Adebowale Ojo ya soke zargin da ake yi wa matashiyar da ke aji shida na sakandare bayan shawarar da ya samu daga hukumar gurfanarwa ta jihar Legas

Wata kotun majistare da ke jihar Legas ta saki wata matashiyar budurwa mai shekaru 15 da ta kashe wani tsoho mai shekaru 51 mai suna Babatunde Ishola.

Matashiyar budurwar ta tabbatar da cewa kare kanta ta yi yunkurin yi bayan tsohon ya yi yunkurin yi mata fyade.

Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade

Kotu ta saki matashiyar da ta kashe tsoho da yayi yunkurin yi mata fyade Hoto: Thisdaylive
Source: UGC

Mai shari'a Philip Adebowale Ojo ya soke zargin da ake yi wa matashiyar da ke aji shida na sakandare bayan shawarar da ya samu daga hukumar gurfanarwa ta jihar Legas.

Daraktan ofishin kare kai na jihar Legas, Dr. Babajide Martins, wanda ofishinsa ya kare matashiyar ya nuna gamsuwarsa a kan hukuncin kotun.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Majalisa ta musanta umartar EFCC da ta binciki ministan Buhari

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani matashi mai shekaru 26 ya tsallaka rijiya da baya a cikin kwanakin karshen mako bayan da ya lalata yarinya mai shekaru bakwai.

Fusatattun mazauna kauyen Akparoji da ke yankin Owukpa na karamar hukumar Ogabdigbo na jihar Benue ne suka yi yunkurin banka masa wuta.

Jaridar Daily Trust ta gano cewa, an kama mutumin mai suna Patrick Onoja Igah yana lalata da yarinya mai shekaru bakwai a farfajiyar coci.

Mazauna yankin sun ce, Ogah wanda aka fi sani da Omolomo, dan asalin Ogwurute Itabono ne a Owukpa. An yi mishi dukan kawo wuka har an kusan kashe shi kafin 'yan banga su kwace shi tare da mika shi hannun 'yan sanda.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Benue, DSP Catherine Anene, ya tabbatar da aukuwar lamarin ga Daily Trust ta wayar tarho. Ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun 'yan sanda.

"Zan iya bada tabbacin cewa matashi mai shekaru 26 da aka kama da laifin yi wa yarinya mai shekaru 7 fyade yana hannun mu," Anene yace.

A cikin kwanakin nan ne jama'a a fadin duniya ke ta cece-kuce a kan yawaitar cin zarafin kananan yara da yi wa 'yan mata fyade da ya yawaita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel