Yanzu-yanzu: Majalisar tarayya ta aminta da sabon kasafin kudin 2020 tare da bashin $5.5bn

Yanzu-yanzu: Majalisar tarayya ta aminta da sabon kasafin kudin 2020 tare da bashin $5.5bn

Majalisar wakilan kasar nan ta amince da gyararren kasafin kudin 2020 inda ta kara shi daga N10.5 tiriliyan zuwa N10.8 tiriliyan.

Duk da cewa kwamitin kula da kasafin kudin wanda rahotonsu aka yi amfani da shi a majalisar a ranar Laraba, sun bukaci a yi amfani da N10,801,544,664,642.

'Yan majalisar sun kara da naira biliyan hudu na walwalar kungiyar likitoci masu neman kwarewa bayan barazanar yajin aiki da suka yi.

Hakazalika, majalisar ta amincewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aro kudi har dala biliyan 5.513 don amfanin kasar nan.

Karin bayani na tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel