Za a gurfanar da mutumin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano - Rundunar 'yan sanda

Za a gurfanar da mutumin da ya yi wa mata 40 fyade a Kano - Rundunar 'yan sanda

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano, ta ce nan ba da dadewa ba za ta tsayar da mutumin nan da ta cafke bisa zargin yi wa mata 40 fyade a gaban Kuliya.

ASP Abdullahi Kiyawa, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, shi ne ya labartawa manema labarai hakan cikin wata sanarwa da ya gabatar a ranar Talata, 9 ga watan Yuni.

A ranar Talata ne dai rundunar 'yan sandan ta kama matashin dan shekaru 32 mai suna, Muhammad Zulfara'u Alfa, a garin Kwanar Dangora da ke wajen birnin Kano.

Matashin yayin amsa laifinsa, ya ce ya yi wa fiye da mata 40 fyade cikin shekara guda ciki har da wata dattijuwa 'yar shekaru 80 a duniya.

Mai Siket
Hakkin mallakar Hoto: BBC

Mai Siket Hakkin mallakar Hoto: BBC
Source: Twitter

Rundunar 'yan sandan ta bayyana cewa, ta kwana biyu tana farautar matashin wanda ya yi kaurin suna wajen yi wa mata fyade kuma aka fi saninsa da Mai Siket.

Kiyawa ya ce matashin wanda ya addabi matan aure da 'yan mata da fyade a Kwanar Dangora ya ce shi da kansa ne yake wannan ta'ada ba tare da hadin bakin wasu ba.

KARANTA KUMA: Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa a fadar shugaban kasa

Ya saba aikata wannan mummunar ta'adi ta hanyar haura katanga domin shiga gidaje masu mata musamman da daddare a lokacin da ya fahimci cewa sun kashe fitulu domin kwanciyar bacci.

Mai Siket ya kuma bayyana wa rundunar 'yan sandan cewa, tabbas laifin da ake zarginsa gaskiya ne kuma har 'yan mata wadanda ba su wuce shekaru 10 ba a duniya ya yi lalata da su.

DUBA WANNAN: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka ana wallafawa

Wata mata mai suna Halima Sani da ke zama a Kwanar Dangora ta shaidawa manema labarai cewa, a yanzu 'yan mata za su iya bacci da ido biyu yayin da Mai Siket ya shiga hannu.

Kansilan Unguwar Yalwa da ke Kwanar Dangora, ya ce sun yi farin cikin da Mai Siket ya shiga hannu saboda ta'adarsa ta janyo lalacewar auren mata da dama.

Ya na mai cewa, al'umma musamman mata a Kwanar Dangora suna farin ciki da safiyar ranar Talata bayan samun rahoton cewa dubun Mai Siket ta cika.

A cewar ASP Kiyawa, "Da zarar mun kammala bincike a kansa za mu mika shi a gaban kotu domin ya girbe abin da ya shuka."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel