Gudaji: Ka da a kashe masu fyade, a tuge masu zakari domin su zama darasi

Gudaji: Ka da a kashe masu fyade, a tuge masu zakari domin su zama darasi

‘Dan majalisar Jigawa, Honarabul Muhammad Gudaji Kazaure, ya yi magana game da fyade da ake yawan yi a Najeriya, ya bada shawarar hukuncin da ya kamata hukuma ta rika dauka.

Muhammad Gudaji Kazaure ya ce: “Duk mutumin da aka kama ya yi wa mace fyade, ka da a kashe shi, amma a yanke zakarinsa. Idan aka cire masa (al’aurar) ba zai sake zuwa ya yi wa wata mata fyade ba. Kuma wannan zai tsaya a zuciyarsa domin zai cigaba da rayuwa ba tare da mazakuta ba.”

“Kuma duk namijin da ya ke rayuwa babu mazakuta, ba namiji ba ne. Idan wani ya na tunanin yin (fyade), ya ga irin wannan hukunci, ba zai soma ba.” Inji ‘dan majalisar tarayyar.

‘Dan siyasar ya ke cewa amma idan aka cigaba da wasa da wannan lamari kamar ba komai ba, za a cigaba da samun karuwar fyade a kasar.

Wasu su na ganin ya kamata a nemi hukuncin da ya dace da macen da aka kama ta yi fyade.

“Ta ya za a ayi wa namiji fyade? Zai yi wahala mace ta yi wa namiji fyade.”

KU KARANTA: Duk inda na shiga na yi magana da Turanci ana ganewa - Gudaji Kazaure

“An ce ana yi wa wasu maza fyade, amma da wuya ayi wa namiji fyade. Saboda kundin tsarin mulki bai ambaci batun yi wa namiji fyade ba. Don haka ne wani ya fara kawo maganar ayi wa tsarin mulkin kwaskwarima.”

“Sai dai abin da na sani a lokacin da mu ke yara, idan namiji ya kutsa cikin dakunan ‘yan mata a makarantar kwana wadanda su ka shafe wata da watanni cikin bukata, za su iya kama ka cikin sauki a nan, har sai ka gamsar da su. Na yarda da wannan.”

“Wannan ba fyade ba ne, za su shawo kanka ne, domin mata su na da hanyar da za su shawo kan mutum. Mata su na shawo kan maza har su amince su yi amfani da su, amma namiji kam karfin tsiya ya ke nunawa, ya yi latata.”

Kazaure ya ce wasu mazan kan yi amfani da makamai domin su cin ma bukatarsu, a wani lokaci mazaje goma su kan yi wa mace guda fyade. Wannan ya sa ya ce akwai bukatar a yi wani abu.

Da kuma ya ke magana game da sha’anin tsaro, Muhammad Gudaji Kazaure ya ce abin kunya ne ace gwamnan jiha ya je ya na yin sulhu da miyagun ‘yan bindigan da ke kashe jama’a.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel