Gwamnonin Jihohi za su yi taro da Matan Gwamnoni kan matsalar yawaitar fyade

Gwamnonin Jihohi za su yi taro da Matan Gwamnoni kan matsalar yawaitar fyade

A yau Laraba, 10 ga watan Yuni, 2020 ake sa ran cewa gwamnonin jihohi 36 za su zauna da kungiyar NGSF ta iyalan gwamnonin Najeriya a game da batun lalata da ake yi da kananan yara da mata da kuma lamarin fyade.

Shugaban harkokin yada labarai na kungiyar NGF, Abdulrazaque Bello-Barkind ne ya bayyana wannan. Abdulrazaque Bello-Barkindo ya fitar da jawabi ne a madadin kungiyar gwamnonin kasar a ranar Talata.

Bello-Barkindo ya ce lamarin da za a tattauna a kai ya zama ruwan dare a halin yanzu a Najeriya. Barkindo ya ke cewa gwamnonin jihohin za su saurari matsaya da kungiyoyi su ka cin ma wajen kawo karshen wannan matsala.

Haka zalika mai dakin shugaban kungiyar gwamnoni watau uwargidar gwamnan Ekiti, Erelu Bisi Fayemi, za ta yi wa gwamnonin jawabi a wajen wannan taro da za a yi ta kafar yanar gizo.

Jaridar Daily Trust ta ce wannan shi ne taro na goma da za ayi ta yanar gizo tun bayan da annobar COVID-19 ta barke a Najeriya.

KU KARANTA: Fasto ya bayyana a Kotu da laifin yi wa Budurwa fyade a cikin cocinsa

Ministar harkokin mata, Pauline Talen, za ta tofa albarkacin bakinta a wajen ganawar.

Kamar yadda Abdulrazaque Bello-Barkindo ya bayyana, Misis Pauline Talen za ta yi magana ne a game da abin da ya shafi yi wa kananan yara da mata fyade da matsalolin jinsi da ake fuskanta.

Idan ba ku manta ba jama’a su na ta kokawa a dalilin barnar da masu fyade su ke yi a wurare da-dama. Lamarin har ya kai ga kashe wasu mata bayan an yi lalata da su da karfin tsiya a cikin ‘yan kwanakin da su ka wuce.

A makon jiya aka kashe wata Budurwa mai suna Barakat Bello bayan an yi mata fyade a gidan iyayenta. Haka zalika an kashe wata mata mai ciki mai suna Azeezat Shomuyiwa bayan an yi lalata da ita, wannan duk ya faru ne a a jihar Oyo.

Gwamnonin za su kuma tattauna a kan batun tattalin arziki, annobar COVID-19 da sha’anin mulki. Irinsu Nasir El-Rufai da Ifeanyi Okowo za su yi jawabi. Za a fara wannan taro ne da karfe 2:00 na rana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel