Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wani Fasto da ake nema zargin fyade a Jihar Delta

Jami’an ‘Yan Sanda sun kama wani Fasto da ake nema zargin fyade a Jihar Delta

A Ranar Talata, 9 ga watan Yuni, 2020, jami’an ‘yan sanda na shiyyar Warri, jihar Delta, su ka kama shugaban wani coci na Victory Revival Fasting and Prayer Ministry, Bishof Elijah Orhonigbe, bisa zargin yi wa wata Budurwa fyade.

Jaridar The Nation ta boye sunan wannan yarinya mai shekaru 19 da ake zargin faston da yi mata fyade. Ana tuhumar Bishof Elijah Orhonigbe da aikata wannan laifi ne a cikin cocinsa.

Rahotonnin da mu ka samu sun tabbatar da cewa ana tuhumar wannan fasto da aikata danyan aikin ne a ranar Laraba, 20 ga watan Mayu, 2020 a lokacin da ya yi hudubar ceto.

An ba wannan yarinya mai shekara 19 ƙwaya ne kafin ayi amfani da ita kamar yadda aka fadawa hukuma.

Wannan fasto wanda ya shahara a garin Warri ya yi ta ƙoƙarin gujewa faɗawa hannun jami’an tsaro tun bayan da ake fara zarginsa da wannan laifi.

A karshe jami’an ‘yan sanda da ke shiyyar Warri sun yi nasarar cafke wannan limami a ranar Juma’ar da ta gabata.

KU KARANTA: Yadda za ka rika samun labaran Legit.ng Hausa a shafinka da zarar an wallafa

Shugaban dakarun ‘yan sanda na yankin, ACP Mohammed Garba, ya fadawa ‘yan jarida cewa sun kama wanda ake zargin ne bayan mahaifiyar wannan Budurwa ta kai masu kuka.

ACP Garba ya bayyanawa manema labarai cewa mahaifiyar wannan yarinya da aka ketawa alfarma ta na cikin masu yin ibada a wannan coci.

Jami’in ‘yan sandan ya tabbatar da cewa binciken da aka yi ya nuna babu shakka an yi wa wannan budurwa fyade.

Mahaifiyar yarinyar ta ce: “Faston ya yi mafarki cewa mu na cikin matsala a gidanmu, kuma ya zama dole a kawo ‘diyata ya yi mata addu’a kafin mu samu zaman lafiya.”

A dalilin haka wannan mata ta kai ‘Diyar gaban malamin. “Ina tunanin abin da ya faru shi ne, faston ya ba ta ƙwaya kafin ya yi mata fyade. Ni na kai ta asibiti da kai na domin ta shiga gargara na kwana biyu.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel