Bidiyo: Yadda wata mata ta zane diyarta mai shekaru 2 da aka yi wa fyade

Bidiyo: Yadda wata mata ta zane diyarta mai shekaru 2 da aka yi wa fyade

Wata uwa ta fusata 'yan Najeriya bayan faifan bidiyonta tana dukar karamar diyarta da aka yi wa fyade ya karada dandalin sada zumunta.

Matar ta zane karamar diyarta mai shekaru biyu tare da kiranta karuwa saboda ta bari an yi mata fyade.

A cewar matar da ta yada faifan bidiyon, ta hadu da matar da kananan 'ya'yanta mata guda biyu a yankin Idumota a garin Legas.

Ta ce ta fara lura taruwar jini a idon daya daga cikin yaran, lamarin da yasa ta tambayi matar abinda ya jawowa yarinyar taruwar jini a ido.

Ta kara da cewa mahaifiyar yaran ta sanar da ita cewa ta bugi yarinyar ne saboda ta bari an yi mata fyade

Mahifiyar yaran ta zargi yarinyar da bayar da kanta ga wanda ya yi mata fyaden, saboda kullum tana ficewa daga gida zuwa wurinsa.

Da aka tambayeta wanne hukunci ta dauka a kan mutumin da ya yi wa yarinyarta fyade, sai ta ce babu komai saboda yarinyar ce mai laifi.

A ranar Lahadi ne karamar ministar birnin tarayya (FCT), Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta bayyana damuwarta a kan samun yawaitar aikata laifin fyade ga 'ya'ya mata tare da yin kiran a fara zartar da hukunci mai tsauri a kan mazan da aka samu da aikata laifin fyade.

Dakta Ramatu ta bukaci a samar da dokar da zata bayar da damar 'dandake' mazan da aka samu da laifin aikata fyade.

DUBA WANNAN: Babu wata rufa - rufa: APC ta like fom din 'yan takarar gwamnan jihar Edo 6 a allon bango

Ministar ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala rabon kayan tallafi ga gamayyar kungiyoyin matan Abuja (NCWS) da sauran wasu kungiyoyi da su ka hada da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen Abuja.

A cewar ministar, hukumar FCT na aiki tare da hukumar hana safara da fataucin mutane (NAPTIP) domin tabbatar da cewa an fara hukunci mai tsanani a kan ma su aikata fyade, musamman a kan kananan yara.

Dakta Ramatu ta ce bai kamata a zartar da hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifin aikata fyade ba, saboda idan ya mutu ba zai ke jin zafin hukuncin da aka yanke masa ba.

A cewarta, gara a dandake mutum ta yadda zai mutu da bakin cikin cewa ba zai kara samun damar aikata laifi mai kama da fyade ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel