Ya kamata a fara 'dandake' mazan da aka samu da laifin aikata fyade - Ministar Buhari

Ya kamata a fara 'dandake' mazan da aka samu da laifin aikata fyade - Ministar Buhari

Karamar ministar birnin tarayya (FCT), Abuja, Dakta Ramatu Aliyu, ta bayyana damuwarta a kan samun yawaitar aikata laifin fyade ga 'ya'ya mata tare da yin kiran a fara zartar da hukunci mai tsauri a kan mazan da aka samu da aikata laifin fyade.

Dakta Ramatu ta bukaci a samar da dokar da zata bayar da damar 'dandake' mazan da aka samu da laifin aikata fyade.

Ministar ta bayyana hakan ne jim kadan bayan kammala rabon kayan tallafi ga gamayyar kungiyoyin matan Abuja (NCWS) da sauran wasu kungiyoyi da su ka hada da kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen Abuja.

A cewar ministar, hukumar FCT na aiki tare da hukumar hana safara da fataucin mutane (NAPTIP) domin tabbatar da cewa an fara hukunci mai tsanani a kan ma su aikata fyade, musamman a kan kananan yara.

Dakta Ramatu ta ce bai kamata a zartar da hukuncin kisa ga wanda aka samu da laifin aikata fyade ba, saboda idan ya mutu ba zai ke jin zafin hukuncin da aka yanke masa ba.

A cewarta, gara a dandake mutum ta yadda zai mutu da bakin cikin cewa ba zai kara samun damar aikata laifi mai kama da fyade ba.

Ya kamata a fara 'dandake' mazan da aka samu da laifin aikata fyade - Ministar Buhari

Dakta Ramatu Aliyu
Source: UGC

A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta ki amincewa da dokar neman zartar da hukuncin 'dandake' wadanda aka samu da laifin aikata fyade.

Mambobin majalisar sun nuna rashin amincewarsu da dokar yayin tattauna yawaitar aikata fyade ga mata a zaman majalisar na ranar Alhamis.

DUBA WANNAN: NAHCON ta yi karin haske a kan yiwuwar yadda za a gudanar da aikin Hajin bana

Mista James Faleke, mamba a majalisar wakilai daga jihar Legas, ya nemi majalisar ta amince da hukuncin 'dandake' duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Tun kafin ya tambayi ra'ayin sauran mambobin majalisar, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya tambayi Faleke cewa; "me zai faru ga babbar macen da ta yi wa karamin yaro fyade?"

Tambayar ta Gbajabiamila ta haifar da barkewar surutu a zauren majalisar.

Bayan ya tambayi ra'ayin 'yan majalisar a kan dokar, sai su ka yi ihun ba su amince da ita ba.

Duk da haka, majalisar ta saka dokar ta baci a kan yawaitar aikata fyade ga 'ya'ya mata tare da neman zartar da hukuncin daurin rai da rai ga ma su aikata laifin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel