Dan majalisar tarayya ya yi nadamar furucinsa a kan fyade

Dan majalisar tarayya ya yi nadamar furucinsa a kan fyade

Dan majalisar wakilai, Ahmed Jaha dan asalin jam'iyyar APC daga jihar Borno, ya ce ya yi nadamar gatsalin da ya yi wa mata a kan fyade a majalisar yayin da ake tafka muhawara a ranar Alhamis.

Ya nemi yafiyar 'yan Najeriya, ballantana mata.

A wata tattaunawa da Jaha ya yi da manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ya tuna da tsokacin da ya yi ga mata a zauren majalisa inda ya bukacesu da su koyi dabi'ar shigar mutunci don gujewa fyade ko cin zarafi daga mazan da basu iya saisaita kansu.

A makonni da suka gabata, 'yan Najeriya na ta magana a kan yadda al'amarin fyade ya yawaita tare da cin zarafin kananan yara.

A kalla mata biyu aka kashe a makonni da suka gabata bayan an yi musu fyade, lamarin da har yanzu 'yan sanda ke bincika.

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Chibok, Damboa da Gwoza a tarayya, ya ce ya yi nadamar wannan maganar da yayi don ta matukar tunzura mata.

"Na yi kuskuren da ya tunzura mata a Najeriya da 'yan Najeriya baki daya. Ina mika ban hakuri ga iyayenmu mata, matanmu na aure, kanninmu mata da 'ya'yanmu mata.

"Har yanzu ina kan baka na na bada shawarar a kashe duk wanda ya yi fyade, ina nadamar inda na kalubalanci shigar matan.

"Ina bada hakuri saboda na ga wasu na cece-kuce a kan tsokaci na.

"Bana goyon bayan fyade don kuwa ni matsayata shine a kashe duk wanda aka kama da laifin fyade," Jaha yace.

Dan majalisar tarayya ya yi nadamar furucinsa a kan fyade

Dan majalisar tarayya ya yi nadamar furucinsa a kan fyade. Hoto daga The Cable
Source: UGC

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Dan majalisar ya ce, a matsayin sa na dan Adam, dole ne ya yi kuskure wani lokaci.

Kamar yadda yace, kuskure ana yin shi ne ga wanda ya yi wani kokari amma bai fahimci lamarin ba. Daga nan ta rage ga mutum ya karba gyara, ya bada hakuri tare da tuba na har abada, yace.

Jaha ya ce babu wata irin shigar mace da zai sa a yi mata fyade, ganin cewa mata da ke da rauni su ke kawar da kansu daga sha'awa amma maza na kasa yin hakan.

"Na san alhakin duk wani namiji nagari ne ya kare martabar mace.

"Da yawan mata an haifesu da juriya wacce daga Allah take. Saboda haka ne suke iya haihuwa, tsayawa a kan tarbiya, kula da 'yan uwa tare da neman na kansu.

"Mata na yin komai a kammale. Ina matukar sha'awar hakan saboda na mori gaskiya da rikon amanar mace.

"Ina matukar girmama mace tare da alfahari da ita cike da so da kauna," dan majalisar ya sanar.

Jaha ya mika ban hakurinsa ga abokan aikinsa na majalisa da kuma 'yan mazabarsa wadanda suka fusata da tsokacinsa ballantana mata.

Ya yi kira ga majalisar da ta gaggauta saka dokar hana cin zarafi da duk wani cin mutuncin jinsi a kasar nan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel