Tsohuwa yar shekara 70 ta bayyana yadda matashi yayi mata fyade

Tsohuwa yar shekara 70 ta bayyana yadda matashi yayi mata fyade

Wata tsohuwa tukuf mai shekaru saba'in (70) a duniya dake zamanta a Abule Memode, Ijoko a jihar Ogun, ta bayyana abinda ya faru tsakaninta da wani direban dan shekara 25 ranar Talata.

Tsohuwar ta laburta cewa matashin direban mai suna Wasiu Bankole ya fasa dakinta ne kuma yayi mata fyade.

Jaridar City Round ta samu labarin cewa Bankole, wanda mazaunin unguwar ne yana cikin maye ne lokacin da ya shiga dakin tsohuwar misalin karfe 11 na daren Talata.

Rahoton ya bayyana cewa Bankole ya galabeta ne yayinda take bacci kuma yayi mata fyade.

Tsohuwar ta bayyanawa jaridar Punch cewa Bankole ya hana ta ihu ta hanyar rufe mata baki. Da kyar ta samu ta kwaci kanta.

DUBA WANNAN: Dakarun Sojin Najeriya sun hallaka yan bindiga 70 a Kaduna

A cewarta: "Mutumin (Bankole) ya shigo gidana da dare. Ya fasa cikin dakina yayi min fyade. Ya toshe min baki ta hanyar da ba zan iya ihu ba."

"Ni kadai ce ke gida lokacin; mai haya ta ba ta nan."

"Na yi kokarin kwatan kaina amma ya galabeni. Da kyar ya samu yin ihu kuma wasu suka ji ni suka koreshi."

Manema labarai sun tattaro cewa sai da daya daga cikin makwabtan da suka ceci tsohuwar, Ayoola Oluwasegun, ya bugawa matashin sanda a baya kafin ya rabu da ita.

An ce shi ya kai kara ofishin yan sanda ke Agbado kuma shugaban yan sandan yankin, SP Kuranga Yero, ya jagoranci tawagar yan sanda domin kamoshi.

Bayan kwana daya da nemansa aka damkeshi.

Tsohuwa yar shekara 70 ta bayyana yadda matashi yayi mata fyade

Credit: The Punch
Source: Twitter

TSOKACI: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

Kakakin hukumar yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, ta bayyana ranar Alhamis a jawabin da ta saki cewa matashin ya tabbatar da aikata kaifin.

Tace: "A bincikenmu, abin zargin ya tabbatar da aikata laifin amma ya ce cikin maye ya aikata laifin. An kai tsohuwar asibiti domin dubata."

"Amma, kwamishanan yan sanda, CP Kenneth Ebrimson, ya bada umurnin mayar da wanda ake tuhumar sashen CID domin karin bincike da hukunci."

A hirar da Bankole yayi da wakilin Punch, ya bayyana cewa lallai ya kwankwadi giya amma bai yiwa tsohuwar fyade ba. "Na rantse ban yi jima'i da ita ba," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel