Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fyade babban laifi ne a ko ina a fadin duniyar nan. Mutuwar Uwa Omozuwa mai shekaru 22, wacce aka yi wa fyade da kashe ta farfajiyar coci, tare da mutuwar Barakat Bello a garin Ibadan, duk sun tada hankalin 'yan Najeriya.

Hakazalika, akwai kananan yara masu tarin yawa da ake cin zarafi tare da yi musu fyade

Da yawa daga cikin al'amuran fyade da suka yawaita ana danganta su da rashin tsauraran matakai da ake dauka a kan masu aikata laifin.

Tabarbarewar tarbiya da rashin ingantaccen ilimi da wayar da kai a kan illolin fyade na assasa lamarin.

A cikin shekaru da suka gabata, an zargi wasu fitattun 'yan Najeriya da laifiin fyade kuma kimarsu ta zube a idon jama'a.

Ga wasu daga ciki:

1. Dbanj - Dayo Oyebanjo: An zargi mawakin da yin fyade ne bayan ya yi magana a kan fyaden tare da kira ga gwamnati da ta dauka mataki a shafinsa na Instagram.

Amma kuma abokinsa mai suna Ese ya tabbatar da cewa mawakin ya yi wa wata kawarsa fyade.

Sun hadu ne a wata liyafa da aka hada a Legas. Mawakin ya ba wa budurwar kudi don ya kwanta da ita amma ta ki.

Kamar yadda yace, mawakin ya karba daya makullin dakin otal din budurwar inda ya shiga yayi mata fyade.

Har yanzu dai mawakin bai yi martani a kan zargin ba.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

2. Bryomo - Olawale Oloforo: Wata masoyiyar mawakin ta kai masa ziyara a gidansa tare da kawarta. Mawakin bai sassauta ba sai da ya yi mata fyade tare da yunkurin kwanciya da kawarta.

Bayan kwanaki, Brymo ya musanta zargin tare da cewa karya aka yi masa. Ya bukaci mai zarginsa da ta fito fili.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

3. Kwamishinan ruwa na jihar Kogi, Abdulmumin Danga: Wata mata mai suna Elizabeth Oyeniyi ta zargi kwamishinan ruwa na jihar Kogi, Abdulmumini Danga da yi mata fyade.

A wani bidiyo da ya yadu, Oyeniyi ta zargi kwamishinan da sace ta bayan yin wata wallafa a shafinta na Facebook.

Gwamna Yahaya ya bada umarnin bincikar kwamishinan.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

4. MC Galaxy - Innocent Udeme Udofot: A watan Yulin 2019, jaruma Simbee Davis ta zargi mawakin da yi mata fyade a shekaru 9 da suka gabata.

Ta yi bayanin zancen fyaden ne bayan Timi Dakolo ta zargi Fasto Biodun Fatoyinbo a shekarar da ta gabata.

Ta ce mawakin ya yi mata fyade ta hanyar mata barazana da wuka tare da bata magani don hana ta daukar ciki.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

5. Biodun Fatoyinbo da Busola Dakolo: Busola matar Timi Dakolo ta zargin faston da yi mata fyade har sau biyu.

Matar mai 'ya'ya uku ta zargi faston da yi mata fyade tun tana da shekaru 16 kuma shi ya fara saninta 'ya mace.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

6. Peruzzi – Okoh Tobechukwu: Wata budurwa mai suna Princess ta wallafa yadda mawakin ya yi mata fyade bayan ta kai masa ziyara kuma ta kwana a gidansa.

Mawakin ya fito ya karyata tare da tabbatar da cewa bai taba yi wa wata fyade ba.

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna)

Fitattun 'yan Najeriya 6 da ake zargi da laifin fyade (Hotuna). Hoto daga The Nation
Source: Twitter

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel