Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutunci

Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutunci

Wasu 'yan majalisa biyu a majalisar wakilai sun bukaci mata a Najeriya da su dinga shigar mutunci don gujewa fyade.

Cin zarafin mata da yi musu fyade ya yawaita a kasar nan. A makon da ya gabata ne aka ruwaito yadda aka yi wa wasu mata uku fyade, lamarin da ya kai ga kisan biyu daga ciki.

A yayin zaman majalisar wakilan a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, Rotinu Agunsoye, dan majalisa mai wakiltar mazabar Kosofe ta jihar Legas, ya mika bukatar hukunta masu yi wa mata fyade a gaban majalisar.

A gudumawar da 'yan majalisar suka bada, da yawa daga cikinsu sun bukaci mummunan hukunci wanda ya hada da kisa ko dandaka ga masu keta haddin mata a fadin kasar nan.

A yayin bada gudumawa a kan bukatar, Henry Okon Archibong, dan majalisa mai wakiltar Itu/Ibiono a Akwa Ibom, ya ce yana goyon bayan hukunta masu fyade amma saka dokar kadai ba za ta shawo kan matsalar ba.

Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutunci

Fyade: Maza ba katakai bane – Yan majalisa sun bukaci mata su dunga shigar mutunci Hoto: Pulse Nigeria
Source: UGC

Pulse Nigeria ta rahoto ida dan majalisar mai shekaru 53 ya ce za a iya danganta tushen fyade da rashin tarbiyar da ya yawaita a kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Iyayenmu sun Gaza, shugabannin addinai sun gaza, makarantu sun gaza tun daga firamare.

"A saboda halin da kasar nan ke ciki, iyaye basu samun lokutan 'ya'yansu. Wannan ne ya kamata ya zama ginshikin tarbiya da horar da maza.

"Idan wannan ginshikin bashi da kyau, babu yadda za a yi al'umma ta ginu," yace.

Archibong ya ce mata ke janyo maza na musu fyade saboda muguwar shigar fidda tsiraici da suke yi.

Ya ce, "Gaskiya bana goyon bayan yi wa mata fyade amma akwai wata magana da mutane na da ke cewa, idan an bi ta barawo, a bi ta mabi sahu.

"Yadda mata ke shigar fidda tsiraici yanzu abun tsoro ce."

A majalisar aka ji wata mace ta ce, "za ku iya rufe idanunku" bayan ya kammala jawabi.

A jawabin dan majalisa mai wakiltar mazabar Damboa/Gwoza/Chibok ta jihar Borno, Ahmed Jaha ya ce a fara jan hankalin mata su dinga shiga ta gari.

"Dole mata su sauya hali wurin yin shiga ta gari don gujewa cin zarafi daga maza. Saboda maza ba itace bane," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel