An kama matashi mai shekaru 25 ya na yi wa dattijuwa mai shekaru 85 fyade a karamar hukumar Rafi

An kama matashi mai shekaru 25 ya na yi wa dattijuwa mai shekaru 85 fyade a karamar hukumar Rafi

Wani matashi mai shekaru 25, Ezekiel Yunana, ya fada komar rundunar 'yan sanda bayan an kama shi da laifin aikata fyade ga wata dattijuwa mai shekaru 85 a karamar hukumar Rafi da ke jihar Neja.

Dattijuwar ta sanar da rundunar 'yan sanda cewa Yunana ya tsallako mata gida tana bacci tare da yin lalata da ita ta karfin tuwo.

Ta bayyana cewa Yunana ya yi barazanar yin garkuwa da ita idan ba ta bashi kudi ba, ita kuma ta ce bata da kudi.

A cewar dattijuwar, Yunana ya dauki lokaci mai tsawo ya na lalata da ita kafin daga bisani wani jikanta, Ishaku Achidawa, ya zo ya ceceta. Ta ce Achidawa ya shaida Yunana.

Da ya ke amsa laifinsa, Yunana ya ce ya aikata fyade ga dattijuwar ne saboda ba ta da kudin da ya nema a hannunta.

Kakakin rundunar 'yan sanda (PPRO), ASP Abiodun Wasiu, ya ce jami'ansu na ofshin Kagara sun samu nasarar kama Yunana bayan dattijuwar da jikanta sun yi korafi.

An kama matashi mai shekaru 25 ya na yi wa dattijuwa mai shekaru 85 fyade a karamar hukumar Rafi

Ezekiel Yunana
Source: UGC

Ya kara da cewa Yunana ya amsa da laifinsa da kansa tare da bayyana cewa nan bada dadewa ba za a tura maganar gaban kotu.

A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta ki amincewa da dokar neman zartar da hukuncin 'dandake' wadanda aka samu da laifin aikata fyade.

DUBA WANNAN: Tsohon gwamnan PDP ya koma jam'iyyarsa bayan ya shafe shekaru 6 a APC

Mambobin majalisar sun nuna rashin amincewarsu da dokar yayin tattauna yawaitar aikata fyade ga mata a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Mista James Faleke, mamba a majalisar wakilai daga jihar Legas, ya nemi majalisar ta amince da hukuncin 'dandake' duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Tun kafin ya tambayi ra'ayin sauran mambobin majalisar, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya tambayi Faleke cewa; "me zai faru ga babbar macen da ta yi wa karamin yaro fyade?"

Tambayar ta Gbajabiamila ta haifar da barkewar surutu a zauren majalisar.

Bayan ya tambayi ra'ayin 'yan majalisar a kan dokar, sai su ka yi ihun ba su amince da ita ba.

Duk da haka, majalisar ta saka dokar ta baci a kan yawaitar aikata fyade ga 'ya'ya mata tare da neman zartar da hukuncin daurin rai da rai ga ma su aikata laifin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel