Majalisa ta ki yarda da hukuncin 'dandake' ma su fyade

Majalisa ta ki yarda da hukuncin 'dandake' ma su fyade

Majalisar wakilai ta ki amincewa da dokar neman zartar da hukuncin 'dandake' wadanda aka samu da laifin aikata fyade.

Mambobin majalisar sun nuna rashin amincewarsu da dokar yayin tattauna yawaitar aikata fyade ga mata a zaman majalisar na ranar Alhamis.

Mista James Faleke, mamba a majalisar wakilai daga jihar Legas, ya nemi majalisar ta amince da hukuncin 'dandake' duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.

Tun kafin ya tambayi ra'ayin sauran mambobin majalisar, Femi Gbajabiamila, kakakin majalisar wakilai, ya tambayi Faleke cewa; "me zai faru ga babbar macen da ta yi wa karamin yaro fyade?"

Tambayar ta Gbajabiamila ta haifar da barkewar surutu a zauren majalisar.

Bayan ya tambayi ra'ayin 'yan majalisar a kan dokar, sai su ka yi ihun ba su amince da ita ba.

Duk da haka, majalisar ta saka dokar ta baci a kan yawaitar aikata fyade ga 'ya'ya mata tare da neman zartar da hukuncin daurin rai da rai ga ma su aikata laifin.

A ranar Talata ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aika sakon ta'aziyya ga dangin matashiyar dalibar nan, Uwaila Omozuwa, wacce aka kashe ta hanyar yi ma ta fyade a cikin coci a jihar Edo.

Majalisa ta ki yarda da hukuncin 'dandake' ma su fyade

Majalisa
Source: Twitter

A takaitaccen sakon da ya wallafa a shafinsa na tuwita, shugaba Buhari ya bukaci rundunar 'yan sanda ta gaggauta gudanar da bincike tare da zakulo wadanda su ka yi wa matashiyar kisan gilla.

DUBA WANNAN: Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi

"Ina mai mika sakon ta'aziyya ga dangi da abokan Uwaila Omozuwa. Ina kira ga rundunar 'yan sanda ta Najeriya a kan ta hanzarta yin bincike tare da zakulo duk wani mai hannu a cikin lamarin domin tabbatar da cewa an gurfanar da su a gaban shari'a," a cewar shugaba Buhari.

Rundunar 'yan sandan Najeriya a jihar Edo ta sanar da cewa ta kama wani da ake zargin ya na da hannu a kisan Omozuwa.

A cewar Chidi Nwabuzor, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, an kama mutumin ne bayan zanen yatsunsa sun fito a jikin tukunyar gas da aka yi amfani da ita wajen kisan matashiyar.

Rundunar 'yan sanda ta ce an kaiwa Omozuwa farmaki ne yayin da ta ke karatu a cikin Cocin RCCG (Redeemed Christian Church of God), da ke birnin Benin.

Maigadin dare a Cocin ya zo ya samu Omozuwa kwance a cikin jini, rabin jikita tsirara sakamakon yaga tufafinta da aka yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel