An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi wa 'yar shekara biyu fyade ta mutu a Kaduna

An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi wa 'yar shekara biyu fyade ta mutu a Kaduna

- Babban kotun jihar Kaduna ta zartar wa Usman Shehu Bashir hukuncin kisa ta hanyar rataya

- Hakan na zuwa ne bayan kotun ta tabbatar da laifin yi wa yarinyar yar shekaru biyu fyade da Bashir ya yi

- Lamarin dai ya afku ne tun a ranar 23 ga watan Maris na 2015 amma sai yanzu kotu ta kammala shariar

Babban kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Sabon Gari Zaria, a ranar Laraba ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wani Usman Shehu Bashir da ya yi wa 'yar shekara biyu fyade har ta mutu.

Alkalin kotun, Mai shari'a Kabir Dabo ya ce wanda aka yanke wa hukuncin ya amsa cewa ya aikata laifin, inda ya kara da cewa kamar yadda sashi na 221 na dokar Penal Code ta tanada, ya yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi wa yar shekara biyu fyade ta mutu a Kaduna

An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi wa yar shekara biyu fyade ta mutu a Kaduna. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An kama matashin da ya kashe kaninsa saboda farfesun kayan ciki

An fara sauraron shariar ne tun a ranar 23 ga watan Maris na shekarar 2015 kuma an kwashe shekara biyar ana shariar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai sharia Dabo ya ce, "A ranar da abin ya faru, wanda aka yanke wa hukuncin ya tafi da marigayiya Fatima zuwa dakinsa na tsawon mintuna 40 inda ya yi mata fyade kuma hakan ya yi sanadin mutuwarta."

A wani rahoton, kunji cewa 'yan sanda sun kama wani matashi, Ishaku mai shekaru 21 da haihuwa saboda kashe abokinsa, Zeloti ta hanyar daba masa wuka don rikici a kan budurwa.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a wani mashaya a garin Dass a ranar Juma'a 29 ga watan Mayu inda Ishaku ya caka wa Zeloti wuka har sau uku kan musun da suke yi a kan wanene ainihin saurayin yarinyar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili ya tabbatar da afkuwar lamarin kamar yadda LIB ta ruwaito.

Wakili ya ce an garzaya da Zeloti John zuwa babban asibitin garin Dass inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

An birne shi a ranar 1 ga watan Yunin shekarar 2020.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ya ce an kama wanda ake zargin kuma yana tsare yayinda ake cigaba da binciken gano musababbin mutuwar mammacin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Sabon tsarin Facebook: Yadda zaka rika ganin labaran Legit.ng Hausa a shafinka da dumi-dumi https://hausa.legit.ng/1335587-sabon-tsarin-facebook-yadda-zaka-rika-ganin-labaran-legitng-hausa-a-shafinka-da-dumi-dumi.html

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel