Manchester ta amince da kara wa'adin zaman aron Ighalo a Old Trafford

Manchester ta amince da kara wa'adin zaman aron Ighalo a Old Trafford

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United da ke kasar Ingila ta cimma yarjejeniya da takwararta, Shanghai Shenhua, ta kasar China domin tsawaita zaman aron dan wasan gaba, Odion Ighalo, dan asalin Najeriya.

A yarjejeniya ta farko da aka kulla, kwantiragin zaman aron Ighalo a Manchester United zai kare ne ranar Lahadi, 31 ga watan Mayu, 2020.

Amma, sai gashi kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta sanar a shafinta cewa Ighalo zai cigaba da zama a kungiyar har zuwa watan Janairu na shekarar 2021.

Kungiyar Manchester ta so sayen Ighalo amma farashin da kungiyar Shanghai Shenhua ta nema ya yi mata tsada.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel