Yadda tsoho mai shekaru 57 tare da mutum 10 suka yi wa yarinya fyade

Yadda tsoho mai shekaru 57 tare da mutum 10 suka yi wa yarinya fyade

Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta bayyana yadda tsoho mai shekaru 57 a kauyen Ma'ai da ke karamar hukumar Dutse ta jihar ya hadu da wasu mutane 10 don yi wa yarinya mai shekaru 12 fyade.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, SP Abdu Jinjiri ya tabbatar da kama wadanda ake zargin ga Kamfanin Dillancin Labarai a ranar Lahadi a garin Jigawa.

Jinjiri ya ce wadanda ake zargin an kama su ne a ranar 30 ga watan Mayu a karamar hukumar Dutse ta jihar.

Yadda tsoho mai shekaru 57 tare da mutum 10 suka yi wa yarinya fyade

Yadda tsoho mai shekaru 57 tare da mutum 10 suka yi wa yarinya fyade Hoto: The Sun
Source: UGC

Ya yi bayanin cewa 'yan sanda ne suka samu korafi a kan cewa an ga tsohon mai shekaru 57 a kasuwar Limawa yana kokarin jan yarinyar.

"Ana bincikar zargin fyade da aka yi wa yarinya mai shekaru 12 a kasuwar Limawa wanda tsoho dan shekaru 57 ne yayi.

"Bayan bincikarsa, ya ce akwai wasu maza 11 da suka saba lalata da yarinyar a lokuta daban-daban. A take ya lissafo sunayensu sannan aka je aka damko su," Jinjiri yace.

Ya tabbatar da cewa za a mika wadanda ake zargin gaban kuliya.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe hakimin 'Yantumaki a Katsina

A wani labari na daban, Legit.ng ta kawo a baya cewa wata kotun majistare da ke zama a Kafanchan a jihar Kaduna ta daure wani matashi mai shekaru 35 mai suna Abdullahi Sani tare da budurwarsa mai shekaru 20 bayan kama su da tayi da laifin sata.

Sarah Paul da Abdullahi sun saci kaji 64 wadanda suka dinga yanka wa. Jami'a mai shigar da kara ta bayyana cewa ana tuhumar su da hadin baki wurin aikata laifin na sata.

Hakan ya ci karo da sashi na 58, 332, 270 da 312 na dokokin Penal Code na jihar Kaduna.

Yayin karanto hukuncin, Alkali Michael Bawa, ya yanke wa Abdullahi Sani hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon wata 38. Ita kuwa Sarah ta samu hukunci wata 13 saboda rawar da ta taka wajen aikata laifin.

Alkalin ya kara da cin tarar Abdullahi N600,000 yayin da Sarah za ta biya N200,000 a matsayin diyya, jaridar Aminiya ta Daily trust ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel