COVID:19: Ingila ta haramta jima'i da wanda ba dan gida ba a yayin kulle

COVID:19: Ingila ta haramta jima'i da wanda ba dan gida ba a yayin kulle

Sabuwar dokar kulle ta Ingila ga 'yan kasa ta haramta jima'i da dan waje wanda ba dan gida ba a yayin da gari yake kulle.

A ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2020, gwamnatin Ingila ta bayyana sabuwar dokarta da ta haramta shakatawa da jama'a da ba na gida ba a yayin da dokar kulle ke aiki.

Sabuwar dokar ta ce: "Babu wanda aka amince ya yi wani taro a waje ko a gida wanda ya kai mutum biyu ko fiye."

Da farko, duk wanda ya shiga gidan wani ya take dokar kullen shi ake hukuntawa. Amma a halin yanzu da wanda ya shiga, da wanda aka shigarwa gida duk za a gurfanar dasu tare da hukunta su.

Kamar yadda sabbin dokokin suka bayyana, masu dalili mai karfi ne za a bari su yi taro a cikin gida amma banda saduwa a tsakani. Dalilan sun hada da motsa jiki, kaiwa da kawowar jama'a da kuma masu ayyukan dole.

Sauran jama'ar da za su iya bada dalili sun hada da masu karbar shawarar kula da yara, iyayen da suka rabu amma suna haduwa don ganin 'ya'yansu da kuma masu jana'iza.

An umarci 'yan sandan Ingila da su tarwatsa dukkan taro da suka gani tare da kamasu don karbar tara.

COVID:19: Ingila ta haramta jima'i da wanda ba dan gida ba a yayin kulle

COVID:19: Ingila ta haramta jima'i da wanda ba dan gida ba a yayin kulle. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

KU KARANTA: An tsinta gawar tsohon kwamishinan da 'yan bindiga suka sace a daji

A wani labari na daban, a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2020 ne gwamnatin tarayya ta bada umarnin bude kasuwanni da wuraren bauta a fadin kasar nan.

Gwamnatocin wasu jihohi tuni suka bi dokar, wasu sun ki yayin da wasu har a halin yanzu basu ce komai ba game da dokar.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa , lokacin bude kasuwanni da wuraren bauta a jiharsa bai zo ba.

Kamar yadda gwamnan ya wallafa a shafinsa na twitter, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna bata aminta da bude kasuwanni da wuraren bauta ba.

An rufe wadannan wuraren bautar tun a watan Maris din 2020 a matsayin hanyar dakile yaduwar mummunar annobar korona a jihar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel