Yanzu-yanzu: Jihar Borno ta sallami masu cutar Korona 135

Yanzu-yanzu: Jihar Borno ta sallami masu cutar Korona 135

Gwamnatin jihar Borno karkashin jagorancin gwamna Babagana Umara Zulum, ta sallami masu fama da cutar Coronavirus mai toshe numfashi 135 kawo yanzu, Punch ta ruwaito.

An tabbatar da masu jinyan cutar sun samu sauki ne bayan gwaji biyu daban-daban sun nuna cewa sun barranta daga cutar.

Mataimakin gwamnan jihar, Usman Kadafur, ya bayyana hakan ne ranar Juma'a, 29 ga Mayu, 2020 yayinda ya kai ziyara cibiyar tunawa da Abba Kyari na killace masu cutar Coronavirus.

Ya bayyana irin nasarorin da gwamnatin jihar ta samu wajen yakar cutar kuma ya yabawa kungiyar kiwon lafiyan duniya WHO da abokan arziki.

Mataimakin gwamnan wanda shine shugaban kwamitin yaki da cutar COVID-19 ya siffanta hadin kan gwamnatin da kungiyoyin wajen yakar cutar ta haifi da mai ido.

Kadafur ya shawarci al'ummar jihar da su kasance masu bin dokokin da aka tsara da sharrudan da aka gindaya domin takaita yaduwar cutar da kuma kawar da ita gaba daya.

Yanzu-yanzu: Jihar Borno ta sallami masu cutar Korona 135
Yanzu-yanzu: Jihar Borno ta sallami masu cutar Korona 135
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng