Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mika sabuwar bukatar cin bashi gaban majalisar tarayya

Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari ya mika sabuwar bukatar cin bashi gaban majalisar tarayya

Shugaban kasar Najeriya, Manjo Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya bukaci amincewar majalisar wakilan tarayya a kan karbo sabon bashin $5.513 biliyan.

A wata wasika da kakakin majalisar wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya karanta wa majalaisar daga shugaban kasar a ranar Alhamis, ya ce za a yi amfani da bashin ne wajen cike gibi kasafin kudin 2020, daukar nauyin manyan ayyuka da wasu jihohin kasar nan.

Babu dadewa da majalisar tarayyar kasar nan ta amincewa gwamnatin tarayyar da karbo bashin N850 biliyan, yayin da bukatar amincewa da karbo wani bashin na $22.79 biliyan ke gaban majalisar.

Karin bayani na nan tafe....

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel