Shekaru 10 muka kwashe matata tana yi min fyade - Magidanci

Shekaru 10 muka kwashe matata tana yi min fyade - Magidanci

Sau da yawa idan aka yi zancen fyade ko cin zarafi cikin aure, mata ake saka wa a sahun gaba. Maza na fuskantar cin zarafi a cikin aure amma basu bayyana wa balle su samu taimako.

Ga wani matashi da ya tattauna da BBC a kan halin cin zarafin da ya fuskanta tare da fyade daga matarsa.

Kamar yadda matashin magidancin ya bayyana, ya ce mutane daga waje suna masa kallon komai lafiya don yana wasa da dariya tare da nishadi na rayuwa. Sun zagaye kusan dukkan kasashen duniya tare da matarsa.

Shekaru 10 muka kwashe matata tana yi min fyade - Magidanci

Shekaru 10 muka kwashe matata tana yi min fyade - Magidanci Hoto: Tori News
Source: UGC

Ya ce bata cin zarafinsa matukar suna gaban mutane amma babban tashin hankali shine zamansu su biyu a kadaice.

Ya ce sun hadu da matarsa suna da shekaru 20 da doriya kuma ita ce tace tana sonsa.

"Jima'i na na farko da ita bai yi min dadi ba amma da son rai na aka yi. Jima'in yayi min zafi sosai. Sa'o'i biyar muka shafe muna aiki daya kuma na cutu.

"Ana tarawa ne don jin dadi amma ni ban taba jin dadi sa ba. Ban saba yin jima'i ba kuma duk na wahala. Idan nace mata a'a, bata dainawa sai an yi tunda tana so. Da haka ta fara min fyade," matashin yace.

Ya kara da cewa, "Na tafi da ita wata kasa kasuwanci amma haka ta addabeni. Koda bana so sai anyi. Idan na musanta kuwa sai ta dukeni amma babu matakin da nake iya dauka. Tana amfani da kumba inda take kartar jikin har sai ya fitar da jini. Jikina duk ciwukan ta ne.

"Bana iya dukanta sakamakon tarbiyya da ta nuna min dukan mace ba daidai bane. Na kuma kasa guduwa in barta.

"Na koma gidanmu amma duk kokarina na yanke alakata da ita ya ci tura. Idan mun yi fada nakan kashe wayata kuma na boye amma za ta biyo ni ta bani hakuri tare da alkawarin za ta canza," ya kara da cewa.

"Da kyar na samu muka kai ziyara wurin wani likita mai bai wa jama'a shawarwari inda dukkanmu muka bayyana abinda ke cikinmu. A nan ne na samu damar sanar da cin zarafin da nake ci amma ita ta karyata.

KU KARANTA KUMA: Korona: Mutane 276 un karu a Najeriya, 19 a Kaduna, 4 a Kano

"Ta dinga ihu tana cewa sharri nayi mata tare da bukatar rabuwarmu.

"Ranar da na saka hannu a kan takardun rabuwata da ita shine rana mafi farin ciki a rayuwata."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel