Ba a ga wata ba a Najeriya, Idi sai ranar Lahadi –Sarkin Musulmi
Majalisar Koli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya, NSCIA, ta sanar cewa za a cigaba da azumi a ranar Asabar.
Kwamitin duban wata ta NSCIA ta ce ba a ga wata ba a kasar saboda haka za a cigaba da azumi a ranar Jumaa.
Ta ce za a gudanar da azumi talatin a bana ba kamar yadda wasu musulmi suka fara shirin yin Idi a ranar Asabar ba.
Da ta ke sanar da sakamakon neman watar a ranar Jumaa, ta sanar da cewa "Ba a ga jaririyar watar Shawwal ba a Najeriya, gobe 30 ga watan Ramadan. Za a fitar da sanarwar daga ofishin sarkin musulmi nan ba da dadewa ba."

Asali: UGC
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng