Yanzu-yanzu: Rayuka sun salwanta yayinda motar Bas tayi kicibis da motar Tanka

Yanzu-yanzu: Rayuka sun salwanta yayinda motar Bas tayi kicibis da motar Tanka

Rayuka sun salwanta yayinda da dama sun jikkata a wani mumunan hadarin da ya auku a gadar saman Otedola dake jihar Legas da safiyar Alhamis, 21 ga Mayu, 2020.

Mun tattaro cewa hadarin ya faru ne misalin karfe 8 na safe.

Hukumar kiyaye hadura na jihar Legas, LASTMA, ta bayyana cewa hadarin ya auku ne tsakanin motar Tanka da wata motar Bas mai dauke da fasinjoji 10.

A jawabin da hukumar ta saki, tace: "Mumunan hadari ya auku ne kan gadar Otedola, yayinda ake kokarin shiga Berger tsakanin wata Tanka da motar Bas kirar Mazda."

Saurari cikakken rahoton....

Source: Legit

Tags:
Online view pixel