Karuwar ta'addanci: Fadar shugaban kasa ta yi wa 'yan majalisa martani a kan kokensu

Karuwar ta'addanci: Fadar shugaban kasa ta yi wa 'yan majalisa martani a kan kokensu

Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta tabbatar da cewa za ta shawo kan matsalar tsaro da ke addabar kasar nan.

Garba Shehu, mataimaki na musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, ya tabbatar da cewa kiran da majalisar tarayya ta yi wa shugaban kasar a kan kashe-kashen da ake a jihohin Neja, Zamfara, Kaduna, Sokoto da Kebbi za a dauka mataki.

A ranar 17 ga watan Mayun 2020 ne shugaban kasa Buhari ya umarci rundunar sojin Najeriya da su gaggauta share 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ke addabar jihohin arewan.

Shehu yace: "Runduna ta musamman ta jami'an tsaro a halin yanzu sun tunkari 'yan ta'addan. Tawagar tsaro suna jihohin don dubawa tare da gano inda za su mamaye".

A zaman zauren majalisa na ranar Talata, an jinjinawa shugaba Buhari a kan umarnin da ya bada na gaggauta kawar da 'yan bindigar jihar Katsina.

Jinjinar ta biyo bayan bukatar da wani dan majalisar ya mika na hadin kai tsakanin jihohin Niger, Zamfara, Kaduna, Kebbi da Sokoto.

Karuwar ta'addanci: Fadar shugaban kasa ta yi wa 'yan majalisa martani a kan kokensu

Karuwar ta'addanci: Fadar shugaban kasa ta yi wa 'yan majalisa martani a kan kokensu. Hoto daga Daily Nigerian
Source: Facebook

KU KARANTA: Bude masallatai: Majalisar malaman Kano ta yi zazzafan martani ga Ganduje

Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya mika bukatar gaban majalisar.

Amma kuma, hadimin shugaban kasar ya ce gwamnatin shugaba Buhari ba za ta sa wata jiha ta jigata ba duk da banbancin siyasa da gwamnatoci.

A halin yanzu, ma'aikatar tsaro ta shirya tsaf don kaddamar da "Operation Accord" don gaggauta kawo karshen ta'addanci a jihohin Kaduna, Niger, Katsina, Zamfara, Sokoto da sassan jihar Kebbi.

A wani labari na daban, majalisar malaman jihar Kano ta ce kamata yayi gwamnati ta yi tunani kafin yanke hukuncin dawo da gabatar da sallar Juma'a da idi a jihar saboda yuwuwar yaduwar cutar korona.

Mallam Ibrahim Khalil, shugaban kungiyar majalisar malaman Kano, ya sanar da BBC cewa gwamnatin jihar ba ta tuntubesu ba a yayin yanke wannan hukuncin nata. Amma ya kamata a ce ta yi la'akari da bukatar jama'a.

Kamar yadda malamin ya bayyana, ya ce ya zama dole a kan gwamnati ta duba damuwar jama'arta da kuma abinda ya dace, tunda bata tuntubi majalisar malamai ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel