Yadda wata karuwa ta wurgo kwastoma ta tagar otal sanye da kwaroron roba (Bidiyo)

Yadda wata karuwa ta wurgo kwastoma ta tagar otal sanye da kwaroron roba (Bidiyo)

'Yan sandan yankin Asokwa da ke kasar Ghana sun kama wasu karuwai 11 bayan an zargi daya daga cikinsu da laifin turo kwastomanta ta tagar otal a Kumasi.

Lamarin ya faru a ranar Lahadi, 10 ga watan Mayun 2020 a otal din Anidaso da ke birnin Kumasi a yankin Ashanti. Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar mutumin.

Wanda ya mutu yana cikin shakrunsa na 30 kuma an zarga turo shi aka yi daga tagar bayan ya je rage zafi a wurin daya daga cikin karuwan.

Wani ganau ba jiyau ba, ya ce an ga mutumin tsirara yayin da ya fado daga tagar har zuwa isowarsa kasa inda ya mutu sanye da kwararon roba.

Masu wucewa sun ce sun fara jin tashin muryoyi daga otal din amma sun zata hirar karuwan ce kamar yadda suka saba amma sai labari ya sha banban.

Binciken farko da 'yan sandan suka fara, ya bayyana cewa mutumin ba kwastoman kullum bane a otal din kuma ya yi barazanar kashe karuwar tun farko.

A yayin zantawa da Joy News, SP Christopher Owusu Mpianin, kwamandan 'yan sandan yankin Asokwa, ya tabbatar da cewa 'yan sanda na binciken yadda mutumin ya mutu.

An mika gawar mutumin zuwa ma'adanar gawawwaki da ke asibitin koyarwa na Komfo Anokye don bincikar abinda ya yi ajalinsa.

KU KARANTA: Kashe-kashen 'yan bindiga: Yadda dan majalisa ya fashe da kuka a yayin zaman majalisa

A wani labari na daban, mataimakin kakakin majalisar jihar Katsina, Shehu Tafoki ya samu damar yi wa zauren majalisa jawabi amma sai ya fashe da kuka a kan rashin tsaron da ya addabi mazabar Faskari.

Yankunan sun saba samun hare-haren 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane da duk wani nau'in rashin tsaro.

A makon da ya gabata, mutum biyar suka halaka sakamakon hare-haren da aka kai a kananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Tafoki, wanda ke wakiltar mazabar Faskari a majalisar jihar, ya ce ba a samun rana daya a halin yanzu da za ta wuce ba tare da an ji harin da aka kai yankin ba.

Kamar yadda yace, karamar hukumar Faskari a halin yanzu za a iya kwatanta ta da Maiduguri, "Ko a daren jiya 'yan bindiga sun kai hari garin Daudawa inda suka yi garkuwa da mutum 4 sannan suka raunata wasu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel