Yanzu-yanzu: Ana artabu tsakanin Soji da yan Boko Haram yanzu haka
1 - tsawon mintuna
Dakarun sojin Najeriya dake zaune a Mainok, jihar Borno yanzu haka na artabu da yan kungiyar tada kayar bayan Boko Haram.
TheCable ta ruwaito cewa yan ta'addan sun dira kauyen ne misalin karfe 7 na yamma sun harbin kan mai uwa da wabi.
Majiya yace: "Sun tafi barikin Sojoji kuma na kusan tsawon awa daya yanzu, suna musayar wuta da Sojin,"
A Febrairu, Sojoji bakwai sun rasa rayukansu yayinda yan ta'addan suka kai hari kauyen.
Saurari cikakken rahoton....
Asali: Legit.ng