Yanzu-yanzu: Magajin kujeran Abba Kyari, Farfesa Gambari, ya dira fadar shugaban kasa
1 - tsawon mintuna
Farfesa Ibrahim Gambari ya dira fadar shugaban kasa, Aso Villa dake birnin tarayya Abuja.
Ya isa kimanin karfe 11 saura yan mintuna da safen nan.
Rahotanni sun bayyana ranar Talata cewa Farfesa Gambari ne shugaba Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban ma'aikatan fadarsa.
Zai maye gurbin Malam Abba Kyari da ya rasu a watan Afrilu bayan fama da cutar COVID19.

Asali: Twitter

Asali: Twitter
Asali: Legit.ng