Da duminsa: An samu mutuwar farfesa na bakwai a jihar Kano cikin yan kwanaki

Da duminsa: An samu mutuwar farfesa na bakwai a jihar Kano cikin yan kwanaki

Wani hazikin malami a jami'ar Bayero dake Kano BUK, Farfesa Monsuru Lasun-Eniola, ya rigamu gidan gaskiya.

Farfesa Lasun-Eniola, wanda kwararren ne a ilmin motsa jiki, ya rasu ranar Laraba a asibitin jami'ar bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi fama shi.

Mr Lasun-Eniola, asalin dan jihar Oyo, ya kasance babban Malami a tsangayar ilmin koyarwa na jami'ar.

Yayinda ake sanar da mutuwarsa da safiyar yau Alhamis, wani babban malami a jami'ar, Garba Sheka, ya siffanta marigayin matsayin mutammasikin Musulmi.

Ba a bayyana irin rashin lafiyan da yayi fama da shi ba.

Abinda ya zahara shine jihar Kano tayi rashin manyan mutane tun lokacin da aka sanar da bullar muguwar cuta mai toshe numfashi watau Coronavirus a jihar.

Mace-macen sun hada mutuwar farfeshoshi bakwai, tsohon babban Alkalin kotun musuluncin jihar, tsohon shugaban hukumar ilmin fari SUBEB, tsohon kwamishanan ilimi, tsohon editan jaridar Triumph da sauran su.

Da duminsa: An samu mutuwar farfesa na bakwai a jihar Kano cikin yan kwanaki
monsuru
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel