COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya

COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya

Ma'aikatan lafiya na kasar Jamus sun wallafa hotunansu tsirara don janyo hankulan gwamnati a kan shiga sahun gaba da suke wajen yakar annobar COVID-19 amma babu kayan kariya.

Kamar yadda jaridar The Nation Online ta ruwaito, kungiyar mai suna Blanke Bedenken ta kafu ne don kira ga ministan lafiya na kasar Jamus a kan halin da suke ciki na wata da watanni.

Sun ce, "idan kayayyakin kariya suka kare mana, haka muke komawa. Wannan ne halin da muke ciki a yanzu da bamu da kayayyakin kariya, tamkar tsirara muke."

Arztezeitung ta wallafa: "Wannan tsiraicin na nuna yadda cutar za ta iya kama mu kenan ba tare da kariya ba."

'Yan kungiyar sun ce suna kallon kansu ne a matsayin wadanda za su iya kamuwa da cutar coronavirus tunda tun a watan Janairu suke bayyana bukatar kayan.

COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya

COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya
Source: Twitter

KU KARANTA: COVID-19: Ganduje ya bayyana yadda cutar ke yaduwa a jihar Kano

Masana'antun da ke samar da kayayyakin sun kara yawan kayan da suke samarwa amma duk da haka basu cimma bukatar ma'aikatan ba.

Takunkumin tace numfashi, safunan hannu da kayan kariya na daga cikin abubuwan da ma'aikatan lafiya da asibitoci ke bukata amma kuma ba a samu.

COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya

COVID-19: Likitoci sun yi zanga-zanga tsirara saboda rashin kayayyakin kariya
Source: Twitter

Gwamnatin jihar Kaduna ta damke wani malamin tsangaya mai suna Aliyu Maikwari a karamar hukumar Zaria.

An zargi malamin ne da cudanya yara maza da mata don almajiranci, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnatin jihar ta kwashe almajirai 327 daga cikin 500 da ke gidansa inda ya basu masauki. Kwamishinan walwala ta jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Baba, ta bayyana hakan ga manema labarai.

Ta ce daga cikin almajiran, akwai 17 duk yara mata ne masu shekaru 8 zuwa 10 kuma an cudanya su ne da sauran kattin almajirai maza a gida daya.

Ta bayyana cewa wannan ba koyarwar addinin Islama bace tare da dora laifin a kan iyayen yara matan da suka kai yaransu.

Ta ce an kama malamin ne a cikin kokarin gwamnatin jihar na mayar da almajirai garuruwansu don hana yaduwar cutar COVID-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel