Yanzu-yanzu: Sabbin mutane 91 sun kamu da Coronavirus ranar Lahadi
1 - tsawon mintuna
Cibiyar hana yaduwar cututtuka a Najeriya watau NCDC ta sanar da samun karin mutane 91 da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 26 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An samu karin mutane tis'in da daya (91) sun kamu da #COVID19"
43-Lagos
8-Sokoto
6-Taraba
5-Kaduna
5-Gombe
3-Ondo
3-FCT
3-Edo
3-Oyo
3-Rivers
3-Bauchi
2-Osun
1-Akwa Ibom
1-Bayelsa
1-Ebonyi
1-Kebbi
A dai-dai karfe 11:50 na daren 26 ga Afrilu, mutane 1273 suka kamu da cutar COVID-19 a Najeriya
An sallami: 239
An samu mutuwa: 40
Asali: Legit.ng