Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya

Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga gwamnatin Najeriya

Shugaban 'yan ta'addan Boko Haram, Abubakar Shekau yana tunanin yada makamai tare da mika kansa ga gwamnatin Najeriya, majiya mai karfi ta sirri daga yankin Arewa maso gabas din kasar nan ta sanar da jaridar The Vanguard.

Majiyar ta sanar da jaridar cewa, Shekau ya fada neman hanya mai sauki don mika kanshi ga gwamnatin.

Kamar yadda majiyar tace, shugaban Boko Haram din ya fara tuntubar wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen duniya don samun ragwame daga gwamnatin Najeriya.

"Ina tsammanin Boko Haram ta kusa zuwa karshe don Shekau na kokarin mika kansa ga hukumomi a Najeriya.

"Ya kagara kuma akwai tabbacin cewa tsananta harin da dakarun kasar nan ke kai musu ne ya kawo hakan," majiyar tace.

Majiyar ta kara da cewa, a kwanakin nan dai kungiyar Boko Haram din na fuskantar kalubale mai tarin yawa sakamakon saka su gaba da dakarun sojin kasar nan suka yi.

Kamar yadda majiyar ta bayyana, Shekau na ganin cewa damarsa na niyyar kubce masa.

"Shiryayyun harin da ake ta kaiwa mayakan ta'addancin ne yasa suka rasa wurin gudu balle su tsira.

Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga rundunar sojin Najeriya
Boko Haram: Shekau na kokarin mika kansa ga rundunar sojin Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Mutum 6 a cikin kwamitin yaki da Covid-19 a Kano sun kamu

"Shugaban rundunar sojin Najeriya ya bada umarnin damko masa Shekau da ransa. Shugaban ya koma Borno har sai ya ga karshen ta'addanci.

"Akwai alamun kuwa zaman ya je yi don babu wata alama da ke nuna ya shirya barin garin ba tare da ya cimma manufarsa ba," majiyar tace.

Vanguard ta gano cewa kungiyar Boko Haram ta mika kokon bararta ga wasu kungiyoyin taimakon kai da kai na kasashen ketare don nema mata rangwame wurin gwamnatin Najeriya.

Wani ma'aikaci a wata kungiyar taimakon kai da kai wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce Shekau yana ta tura musu sakonni don su taimaka masa wajen neman rangwame wurin gwamnatin Najeriya.

Kamar yadda ya bayyana, "Da farko mun yi zaton shirme ne amma da lamarin ya ci gaba, dole yasa muka sanar da cibiyoyin tsaro."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel