Coronavirus ta kashe 'yan Najeriya da basu taba mu'amala da mai cutar ko fita kasar waje ba

Coronavirus ta kashe 'yan Najeriya da basu taba mu'amala da mai cutar ko fita kasar waje ba

- Kwamishinan lafiya a jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi, ya sanar da mutuwar karin mutane uku da su ka kamu da cutar covid-19

- Daga cikin mutanen uku akwai wani likita, Dakta Emeka Chugbo, wanda ke aikin duba lafiyar mai dauke da kwayar cutar

- Bincike ya nuna cewa sauran mutane biyun da su ka mutu ba su fita daga Najeriya ko yin mu'amala da mai dauke da cutar ba

Kwamishinan lafiya a jihar Legas, Akin Abayomi, ya ce daga cikin mutane uku da su ka mutu sakamakon kamuwa da cutar covid-19 a jihar akwai wani likita da ke duba mai dauke da kwayar cutar.

Farfesa Abayomi ya ce likitan ya kamu da kwayar cutar ne daga wurin maras lafiyar da ya ke dubawa, yayin da sauran mutane biyun ba a san ta hanyar da su ka kamu da cutar ba.

A cewar Farfesa Abayomi, bincike bai nuna cewa sauran mutanen biyu sun fita kasar waje ko yin mu'amala da mai dauke da kwayar cutar da aka sani ba.

"Jihar Legas ta sake samun karin mutane uku da su ka mutu sakamakon kamuwa da cutar covid-19.

Coronavirus ta kashe 'yan Najeriya da basu taba mu'amala da mai cutar ko fita kasar waje ba

Farfesa Akin Abayomi
Source: UGC

"Daga cikin mutanen akwai mai shekara 51, 52 da 62. Daga cikin mamatan akwai likita, wanda ya samu kwayar cutar daga wurin wani da ya dawo daga kasar Turai.

"Bincike ya nuna cewa sauran mutane biyun da su ka mutu ba su yi mu'amala da wani mai dauke da kwayar cutar ba.

DUBA WANNAN: Tsohon dan takarar gwamna a Bayelsa ya mutu yayin tiyatar rage kitse

"Sannan babu shaidar cewa sun fita daga Najeriya," a cewar Farfesa Abayomi.

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa likitan, Dakta Emeka Chugbo, ya kamu da kwayar cutar ne bayan an dauki hayarsa don duba lafiyar mai dauke da kwayar cutar.

Wanna shine karo na farko da aka samu rahoton cewar cutar covid-19 ta hallaka mutane uku a rana daya a jihar Legas.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel