Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 5 bayan sun warke daga cutar Coronavirus

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 5 bayan sun warke daga cutar Coronavirus

An sake sallaman mutane biyar daga asibiti a jihar Legas bayan sun samu waraka daga cutar Coronavirus a ranar Lahadi, 12 ga watan Afrilu, 2020.

Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Lahadi.

Ya yi bayanin cewa mara lafiyan sun hada da mata hudu da namiji daya kuma tuni an mayar da su wajen iyalansu.

Gwamna Sanwo-Olu ya ce kawo yanzu gwamnatin jihar tayi jinya kuma ta sallami mutane 55 bayan gwai ya nuna cewa sun barrantu daga cutar ta Coronavirus.

Gwamnan ya yi kira ga mutan jihar suyi zamansu a gida, baiwa juna tazara, tare da tsafta a koda yaushe.

Yace “Yayinda muke murnar bikin Ista, ina mai kawo muku labarin farin ciki daga cibiyoyin killace mara lafiya.“

“A yau mun sake sallamar mutane biyar; mata 4 da namiji 1.“

Yanzu-yanzu: An sake sallaman mutane 5 bayan sun warke daga cutar Coronavirus

cutar Coronavirus
Source: Depositphotos

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel