Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus ta farko a jihar Kano

Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus ta farko a jihar Kano

An samu bullar cutar Coronavirus ta farko a jihar Kano yau Asabar, 11 ga watan Afrilu 2020, kwamishanan lafiyan jihar, Dr Aminu Ibrahim Tsanyawa, ya tabbatar da hakan.

Yanzu haka ana cikin ganawa tsakanin gwamnan da mukarrabansa.

Nan ba da dadewa ba gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, zai yi jawabi ga al'ummar jihar.

A cewar majiya mai siqa, mutumin da ke dauke da cutar wani tsohon jami'in diflomasiyya ne da aka kwantar a wani asibitin kudi a Kano.

An bayyana cewa mutumin ya yi daga Legas zuwa Abuja sannan ya dira a Kano. An gwadashi ne a cibiyar gwajin dake asibitin koyarwan Aminu Kano AKTH.

Tuni an garzaya da shi dakin killace mutane a Kwanar Dawaki.

Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus ta farko a jihar Kano
Yanzu-yanzu: An samu bullar Coronavirus ta farko a jihar Kano
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel