Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe wani dan kasar waje a jahar Lagas

Yanzun-nan: Coronavirus ta kashe wani dan kasar waje a jahar Lagas

Wani dan kasar Birtaniya mai shekara 66 a duniya ya rasu sakamakon cutar coronavirus a jahar Lagas.

Kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi, ne ya bayyana hakan ta shafin Twitter a ranar Laraba, 8 ga watan Afrilu.

Ya kuma tabbatar da cewar yawan wadanda suka kamu da cutar coronavirus a jahar ya karu zuwa 130.

Ya wallafa a shafin Twitter cewa: “Lagas ta sake samun wanda ya mutu sakamakon cutar COVID-19: wani dan kasar Birtaniya mai shekara 66, wanda ya yi tafiya daga Indiya ta Dubai zuwa Lagas a ranar 17 ga watan Maris, 2020.

“Kamar yadda yake a ranar 7 ga watan Afrilu, an samu sabbin mutane 10 da suka kamu da COVID-19. Jimlar wadanda suka kamu da cutar a Lagas ya kama 130.

“An kuma sallami wani mara lafiya bayan ya warke. Hakan na nufin mutane 32 kenan aka sallama.”

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa a shirye take ta kwaso yan Najeriya mazauna kasashen waje zuwa gida Najeriya, amma fa sai an yi musu gwajin Coronavirus, kuma an tabbatar basu dauke da ita.

Punch ta ruwaito gwamnatin ta bayyana haka ne a shafinta na yanar gizo inda ta nemi yan Najeriya mazauna kasashen waje su bayar da bayani game da matsayinsu lafiyarsu dangane da cutar Coronavirus, musamman ga duk masu son a dawo dasu Najeriya.

Dole sai an yi musu gwajin cutar a kasar da suke zama, kuma an basu takarda a hukumance dake tabbatar da basu dauke dac cutar, dole ne su gabatar da wannan takarda a filin jirgi domin a tabbatar da sahihancinsa kafin a kyale su su shiga cikin jirgi.

Haka zalika duk mai son ya dawo gida shi da kansa zai biya kudin jirgi, sa’annan da zarar an sauka a Najeriya za’a killace mutum tsawon kwanaki 14 a duk inda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta ga ya dace.” Inji sanarwar.

Da take tabbatar da batun, mashawarciyar shugaban kasa a kan harkokin kasashen waje, kuma shugabar hukumar dake kula da sha’anin yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri Erewa ta bayyana cewa hakan na cikin tsarin NCDC, kuma dole ne a bi shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel