Da duminsa: Mutane 10 sun sake kamuwa da Coronavirus a Najeriya
1 - tsawon mintuna
Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da cewa an samu karin mutane goma (10) da suka kamu da cutar Coronavirus (#COVID19) a Najeriya a ranar Lahadi, 5 ga Afrilu, 2020.
Cibiyar ta bayyana hakan a shafin ra'ayinta na Tuwita inda tace: “An tabbatar da mutane goma(10) sun kamu da #COVID19 a Najerya, 8 a Legas, 2 a Abuja, 2 a Edo.“
“Kawo karfe 1:15 na ranar 5 ga Afrilu, mutane 224 aka tabbatar sun kamu da COVID19 a Najeriya, an sallami mutane 27 , kuma mutane 5 a rigamu gidan gaskiya.“

Asali: Facebook
Lagos- 115
Abuja- 45
Osun- 20
Oyo- 9
Akwa Ibom- 5
Ogun- 4
Edo- 9
Kaduna- 4
Bauchi- 6
Enugu- 2
Ekiti- 2
Rivers-1
Benue- 1
Ondo- 1
Asali: Legit.ng