Babu kamfanin da muka ba lasisin fara amfani da 5G a yanzu a Najeriya - Pantami

Babu kamfanin da muka ba lasisin fara amfani da 5G a yanzu a Najeriya - Pantami

Gwamnatin Tarayyar najeriya ta bayyana cewa ba ta bawa kamfanonin sadarwar lasisin fara amfani da fasahar intanet ta 5G ba a kasar a cewar ministan sadarawa Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami.

A cikin sanarwar da ya fitar dauke da saka hannunsa a ranar Asabar ya ce kawo yanzu Najeriya ba ta fara amfani da fasahar 5G ba kuma ofishinsa bai bawa kowane kamfani lasisin fara amfani da 5G a kasar ba.

Ya ce an dai yi gwaji ne domin duba tasirin fasahar ga lafiyar 'yan kasar kafin a kai ga matakin amince wa shi ko akasin haka.

Pantami ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ba za ta dauki mataki ba har sai ta tuntuni kwararru game da fashar ta 5G kana ta ji ra'ayin 'yan kasar.

DUBA WANNAN: NCDC ta yi kuskure a sanar da jimillar masu COVID-19 a Najeriya, ta yi gyara

Isa Pantami ya ce, "Bisa bayan da ke kan teburi na, hukumar National Frequency Management Council (NFMC) wadda ni ne shugabancinta, ba ta bayar da izinin kafa fasahar 5G ba a Najeriya."

Ya kara da cewa, "An tsinkayar da ofishina kan wasu bayanai da ke danganta annobar COVID-19 da fasahar 5G a Najeriya. Saboda haka nake so na fayyace cewa har yanzu ba a bayar da lasisin kafa 5G ba a Najeriya."

Wannan na zuwa ne a lokacin da wasu mutane da dama a sassan duniya ke zargin cewa akwai bullar annobar coronavirus yana da alaka da fasahar ta 5G, wadda hakan yasa suka fara lalata turaken layin intanet har da cinna masa wuta a wasu wuraren.

Suma 'yan Najeriya ba a bar su a baya ba a batun inda mutane ke ta bayyana mabanbantan ra'ayinsu game da batun musamman ma a dandalin sada zumunta na Twitter inda ake tattauna batun da maudu'in #5GinNigeria.

Daga karshe Pantami ya ce ya umurci hukumar NCC ta amsa tambayoyin 'yan Najeriya game da sabuwar fasahar ta 5G.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel