Muhammadu Sanusi II da Iyalinsa ba su dauke da COVID – 19 inji ‘Dansa

Muhammadu Sanusi II da Iyalinsa ba su dauke da COVID – 19 inji ‘Dansa

A daidai lokacin da cutar Coronavirus ta ke cigaba da yaduwa a Najeriya, wasu sun fara nuna tashin hankalinsu game da halin da Duniya ta samu kanta.

A dalilin haka ne wasu su ka fara yin kira ga tsohon Sarki, Muhammadu Sanusi II da ya yi maza ya yi gwajin wannan cuta domin ya san halin da ya ke ciki.

Masoya sun bukaci tsohon Sarkin na Kano ya yi wannan gwaji ne sakamakon ganin irin mutanen da su ka rika kawo masa ziyara bayan tube masa rawani.

Wani Bawan Allah ‘Dan asalin jihar Kano, Mahmud Labaran Galadanchi, ya na cikin wadanda su ka fito su ka yi irin wannan kira da babbar murya ga Sanusi II.

A shafinsa ns Tuwita, Mahmud Galadanchi ya rubuta: “Ina tunanin ya kamata Muhammadu Sanusi II ya mika kansa domin ayi masa gwajin cuyar COVID-19…

Ya ce: “Ya karbi bakuncin mutane daga gida da wajen Najeriya bayan an tsige shi daga gadon sarauta. Wadanda su ke kusa da shi, su ba shi shawara don Allah.”

KU KARANTA: Abba Kyari, Bala da El-Rufai sun shiga sahun masu Coronavirus

Bayan ya yi wannan magana a Ranar Asabar, 28 ga Watan Maris, sai daya daga cikin ‘Ya ‘yan tsohon Sarkin ya bada amsa a shafin na Tuwita dazu da Asuba.

Adam Sanusi Lamido wanda aka fi sani da Ashraf Sanusi, ya nuna cewa tuni Mahaifin na sa ya yi wannan gwaji, haka zalika Matansa da kuma sauran ‘Ya ‘yansa.

Ashraf Sanusi ya ce: “Shi (Muhammadu Sanusi II) da sauran ‘Yanuwana da Iyayena da su ke tare da shi duk ba su dauke da wannan cuta. Mun godewa Allah.”

A karshe ya kara da cewa: “Duk da haka mu tabbatar mun cigaba da yi wa marasa lafiya addu’a.” Jama’a sun nuna farin cikinsu da jin wannan labari mai dadi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel