Yanzu-yanzu: Buhari ya karbi bakuncin Ministan Lafiya da Shugaban NCDC (Hotuna)
1 - tsawon mintuna
Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin Ministan kiwon lafiya, Osagie Ehenire da Dirakta Janar na hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya Chikwe Ihekweazu, a fadar shugaban kasa, Aso Villa.
Sun ziyarcesa ranar Asabar ne domin bayyana mai halin da Najeriya ke ciki game da annobar cutar Coronavirus.
Mun kawo muku rahoton cewa Buhari ya koma aiki ofishinsa ranar Laraba kafin aka yi mata feshi ranar Alhamis.
Ba shiga ofis ranar Alhamis da Juma'a ba, yana zaune a gida.
Ana kyautata zaton zai koma aiki ofis makon gobe amma babu tabbacin ranar.

Asali: UGC

Asali: UGC

Asali: UGC
Asali: Legit.ng