Ana iya daukan Coronavirus ta hanyar jima'i - Ministan Lafiya

Ana iya daukan Coronavirus ta hanyar jima'i - Ministan Lafiya

Ministan Lafiya na Najeriya, Osagie Ehanire ya ce akwai yiwuwar za a iya yada kwayar cutar Covid-19 da aka fi sani da Coronavirus ta hanyar jima'i.

Yayin jawabin da ya yi wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, Mista Ehanire ya ce ya yi imanin cewa "idan mutum yana dauke da kwayar cutar ta coronavirsu, zai iya yada wa ta hanyar jima'i."

Sai dai a akwai bukatar da ayi amfani da kimiyya wurin gwaji domin tabbatar da hakan duba da cewa Covid-19 sabon cuta ne kuma har yanzu ana cigaba da bincike domin gano hanyoyin yaduwar cutar.

Ana iya daukan Coronavirus ta hanyar jima'i - Ministan Lafiya

Ana iya daukan Coronavirus ta hanyar jima'i - Ministan Lafiya
Source: UGC

Wasu masu binciken kimiyya sun yi ikirarin cewa ba za a iya yada kwayar cutar da hanyar jima'i ba sai dai kawai ta bakin mutum.

DUBA WANNAN: Rashin iya gamsar da matarsa a wurin kwanciya ya saka wani mutum kashe kansa

Wani mai binciken kimiyya, Jessica Justman da ta yi magana da jaridar Gauradian UK, ya ce a halin yanzu ba su ganin alamun cewa ana iya yada kwayar cutar da hanyar jima'i.

Amma duk da hakan, ta bayar da shawarar idan daya daga cikin ma'aurata ko masoya ya kamu da cutar, zai fi dacewa a kaurace masa domin gudun kamuwa da cutar.

A halin yanzu dai binciken kimiyya ya tabbatar ana iya yada Covid-19 ta hanyar shakar kwayar cutar daga iska idan wani ya yi atishawa ko kuma taba wani abu da mai dauke da cutar ya taba.

Wannan shine dalilin da yasa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran hukumomin lafiya suke bayar shawarar mutane su rika wanke hannunsu da sabulu da ruwa daga lokaci zuwa lokaci ko su rika amfani da sinadarin kashe kwayoyin cuta wato sanitizer.

Ta kuma bayar da shawarar mutane su guji taruwa a wurare da ake cinkoso su kuma rika wanke wurare da sinadarin kashe kwayoyin cuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel