Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

Tun farkon samun bullar kwayar cutar coronavirus a Najeriya ta hannun wani dan kasar Italiya, an tabbatar da samun kwayar cutar a jihohin Najeriya 12.

Ya zuwa yanzu kwayar cutar coronavirus ta hallaka mutane 15,000 a fadin duniya.

Mutum daya ne ya mutu a Najeriya bayan kamuwa da kwayar cutar coronavirus, amma adadin masu dauke da cutar ya kai mutum 96, kamar yadda kididdigar cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa ta kasa (NCDC) ta nuna.

Ga jerin jihohin Najeriya da aka tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus da adadin mutanen da suka kamu da ita;

1. Legas - mutum 59

2. Abuja - mutum 16

3. Ogun - mutum 3

4. Ekiti - mutum 1

5. Edo - mutum 2

6. Bauchi - mutum 2

7. Enugu - mutum 2

8. Oyo - mutum 7

9. Benue - mutum 1

10. Kaduna - mutum 1

11. Ribas - mutum 1

12. Osun - mutum 2

Tuni jihar Legas, da ke da mafi yawan wadanda suka kamu da kwayar cutar, ta bayar da umarnin kasuwannni, ana sa ran rufe kasuwannin ne daga ranar Alhamis.

Jerin jihohin Najeriya 7 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus
Abba Kyari
Asali: Depositphotos

Yawacin mutanen da aka samu da kwayar cutar corona, 'yan Najeriya ne da suka dawo daga kasashen ketare, musamman turai.

An tabbatar da samun kwayar cutar a jikin manyan jami'an gwamnati guda uku.

DUBA WANNAN: Za a yi wa Ali Nuhu da wasu jaruman Kannywood 5 gwajin COVID-19

Shugaban ma'aikatan farar shugaban kasa, Abba Kyari, shine na farko da aka fara samu dauke da kwayar cutar. Na biyu shine gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, sai kuma kakakin majalisar jihar Edo.

Ya zuwa yanzu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati sun killace kansu bayan sun gano cewa sun yi mu'amala da masu dauke da kwayar cutar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel