Yanzu-yanzu: Oshiomole ya bada umurnin kulle shelkwatar APC gaba daya

Yanzu-yanzu: Oshiomole ya bada umurnin kulle shelkwatar APC gaba daya

Shugaban Jamiyyar All Progressive Congress (APC), Kwamred Adams Aliyu Oshiomhole, ya bada umurnin kulle shekwatar jamiyyar dake Abuja saboda cutar Coronavirus.

Ya ce sun yanke shawarar haka ne domin bin umurnin gwamnatin tarayya na hana tara mutane da yawa a wurare.

Yayinda yake magana da manema labarai, Oshiomole ya umurci dukkan ma'aikatan jam'iyyar suyi zamansu a gida kada su yada cutar.

Yace: ” Wannan mataki kiyayewa ne da jamiyyar ta dauka ta hanyar kulle ofishohinta na tsawon makonni biyu saboda a shawo kan lamarin, amma idan yaki ci, yaki cinyewa, zamu tafi hutu ne har sai wani lokaci saboda sai da rai ake aiki.”

Ya tabbatarwa ma'aikatan sakatariyar cewa za a biyasu albashinsu ko sun gida.

Yanzu-yanzu: Oshiomole ya bada umurnin kulle shelkwatar APC gaba daya
Yanzu-yanzu: Oshiomole ya bada umurnin kulle shelkwatar APC gaba daya
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng