Dattijuwa mai shekaru 85 ta daka tsalle daga bene mai hawa hudu ta fado ta mutu

Dattijuwa mai shekaru 85 ta daka tsalle daga bene mai hawa hudu ta fado ta mutu

Wata dattijuwa mai shekaru 85 mai suna Victoria Ilione ta kashe kanta a jihar Anambra kamar yadda rahotani suka bayyana.

Lamarin ya faru ne a unguwar Awada kusa da Onitsa a karamar hukumar Idemili ta Arewa na jihar kamar yadda Punch Metro ta ruwaito.

An gano cewa dattijuwan da kashe kanta ne ta hanyar daka tsalle daga hawa na uku na ginin bene mai hawa hudu.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na jihar, Haruna Mohammed ya tabbatar wa majiyar Legit.ng afkuwar lamarin.

Dattijuwa mai shekaru 85 ta daka tsalla daga bene mai hawa hudu ta fado ta mutu

Dattijuwa mai shekaru 85 ta daka tsalla daga bene mai hawa hudu ta fado ta mutu
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Mohammed ya ce, "Misalin karfe 5.20 na yammacin ranar Talata, an kira ofishin 'yan sanda na Awada cewa wata Victoria Ilione mai shekaru 85 ta daka tsalle daga gidanta da ke hawa na uku a bene mai hawa hudu inda ta ke zaune da diyar ta a gida mai lamba 18 Ilodibe Street, Awada.

"An cewa tsohuwar tana fama da matsalar kwalkwalwa hakan yasa aka takaita mata zirga-zirga. Tana tare da mai kula da ita, Judith Amumuche mai shekaru 32 a gidan lokacin da abin ya faru.

"Sai dai kafin 'yan sanda su isa wurin da abin ya faru, wata Benedicta Ikediaso da ke zaune a rukunin gidaje na 3-3 Onitsha da ake ce diyar matar ne ta dauke gawar amma an ga alamun jini a wurin.

"Mai kula da ita da kuma wasu da abin ya faru a idanunsu suna taimakawa 'yan sanda domin gudanar da bincike."

Kakakin 'yan sandan ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, John Abang ya shawarci dukkan wadanda suka kulawa da mutane su kara takatsantsan domin kare afkuwar irin wannan lamarin mara dadi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel