Jarumin saurayi dan jihar Nasarawa zai auri mata biyu lokaci daya
1 - tsawon mintuna
Wani jarumin saurayi daga karamar hukumar Keana dake jihar Nasarawa, Ibrahim Kasumi Oboshi, wanda aka fi sani da Ogah ya shirya angwancewa da amarensu biyu a rana daya.
Kasimu zai angwance da Nazira Dahiru Ozegya da Rabi Ishaka Akose wacce akafi sani da Talatu ne ranar 28 ga watan Maris 2020.
Za a gudanar da auren farko ne a karamar hukumar Keana ta jihar Nasaraw misalin karfe 10 na safe sannan a garzaya karamar hukumar Obi domin daura na biyu misalin karfe 12.
Allah ya basu zaman lafiya!!

Asali: Facebook

Asali: Facebook
Asali: Legit.ng