Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 5 a Najeriya

Yanzu-yanzu: An samu karin masu cutar Coronavirus 5 a Najeriya

Labarin da ke shigowa da duminsa na nuna cewa an samu karin mutane biyar masu dauke da cutar Coronavirus (COVID-19) a Najeriya, hakan ya kawo adadin yan Najeriya takwas kenan.

Ministn kiwon lafiya, Osagie Ehanire, ya bayyana cewa an samu hudu a Legas, 1 a jihar Ekiti.

Ministan ya kara cewa uku cikinsun sun dawo daga Amurka ne, uwa da diyarta yar mako shida da haihuwa. Sauran biyun kuma daga Ingila suka shigo.

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel