Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

Budurwa ta sa an damke mutumin da ya taba mata nono a motar haya

- Wata budurwa ta bayyana a kafar sada zumuntar zamani yadda ta sa aka kama mata wani mutum da ya taba mata nono a motar haya

- Kamar yadda budurwar ta bayyana aukuwar lamarin, ta ce hakan ya faru ne a safiyar Talata yayin da take bacci a motar haya

- Ta kara da bayyana cewa, bayan 'yan sandan sun kama mutumin ne mutane suka fara rokonta a kan ta kyale shi don ba fyade yayi mata ba

Wata budurwa ta bayyana a kafar sada zumuntar zamani yadda ta sa aka kama mata wani mutum da ya taba mata nono a motar haya.

Kamar yadda budurwar ta bayyana aukuwar lamarin, ta ce hakan ya faru ne a safiyar Talata yayin da take bacci a motar hayar da ta shiga don zuwa Oshodi daga titin Iwo.

Ta kara da bayyana cewa, bayan 'yan sandan sun kama mutumin ne mutane suka fara rokonta a kan ta kyale shi don ba fyade yayi mata ba.

DUBA WANNAN: Kayattacen hoton tsohon Sarki Sanusi da iyalansa bayan saukarsa daga mulki

Ta wallafa a shafinta na twitter cewa, "Idan wani daga cikinku ya san wani mai suna Deji da ya shiga mota daga oshodi zuwa titin Iwo a yau Talata, toh kada a damu don ba zai dawo gida a yau ba ko zuwa wasu kwanaki kadan masu zuwa. Yana lafiya kalau. An dai kama shi ne a kan taba wa mace nono yayin da take bacci a motar haya."

"Zan biya belinsa gobe. Wawan ya ce min mafarki nake yi amma bai taba ba. Fasinjoji kuma sun ce basu ga komai ba. Ni kuma na ji ana taba min jiki bayan ina bacci, koda na bude ido na ga hannayensa a kan nono na. Hakan yasa na fasa ihu." ta kara da cewa.

Kamar yadda tace, "A gaskiya na matukar tsorata. Ga shi nan a halin yanzu yana roko na. Mutane na cewa in kyaleshi don ba fyade yayi min ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel