Yanzu-yanzu: Oshimole ya samu nasara a kotun daukaka kara

Yanzu-yanzu: Oshimole ya samu nasara a kotun daukaka kara

Kotun daukaka kara dake zaune a Abuja ta hana dakatad da Adams Oshiomole a matsayin shugaban jamiyyar All Progressives Congress (APC).

Za ku tuna cewa Alkali Danlami Senchi na babban kotun birnin tarayya dake Jabi Abuja a ranar 4 ga Maris, 2020 ya bada umurnin dakatad da Oshiomole.

Amma kwamitin Alkalan daukaka kara uku karkashin jagorancin, Alkali Abubakar Yahaya, sun yanke hukuncin hana aiwatar da shariar Alkali Danlami Senchi har zuwa ranar Jumaa da za a zauna kan lamarin.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel